Miyagu sun watsa ma wata mata ruwan guba a jahar Katsina

Miyagu sun watsa ma wata mata ruwan guba a jahar Katsina

Wasu gungun miyagu sun watsa ma wata mata, Rabi Ado tare da yayanta biyu ruwan guba, watau Acid, wanda hakan ya yi sanadiyyar kona musu jiki a jahar Katsina, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a gidansu dake Layin Shehii, cikin karamar hukumar Dandume, yayin da Rabi da yayanta, Yahaya Ismail da Zainab Ismail suke kwance sun barci.

KU KARANTA: DSS ta bayyana mutane 2 da suka shirya yi ma Buhari juyin mulki

Rahotanni sun bayyana miyagun sun lallabo ta tagar dakin Rabi ne, inda suka watsa musu ruwan sa’annan suka tsere, a dalilin haka aka garzaya dasu zuwa babban asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Shika Zaria don samun kulawa.

Wani makwabcinsu daya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace su ne suka kai musu dauki yayin da suka jiyo kuwwarsu suna kuka, yace sun tarar da sun samu rauni a bayansu da kafadu da kuma wani yanki na fuskokinsu.

Kaakakin Yansandan jahar Katsina, ASP Anasa Gezawa ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace Yansanda na yin iya bakin kokarinsu don kama wadanda suka aikata wannan mugun aikin. Sai dai yace yan uwan matar sun zargin tsohon mijinta da aikata mata hakan.

“Yan uwan matar suna zargin tsohon mijinta Ismail da wannan laifi sakamakon aurensu ya samu matsala, kuma a yanzu haka maganan na gaban kotu inda take neman kotu ta raba auren. An sanar dashi abin da ya faru ta wayar tarho, amma ya ki zuwa ya dubasu har yanzu.

“Duk da haka mun fara bin diddigin duk inda ya shiga don kama shi.” Inji Gezawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel