Jamilu Abubakar ya yi wa masu surutu a kan Iyalinsa raddi

Jamilu Abubakar ya yi wa masu surutu a kan Iyalinsa raddi

Kyaftin Jamilu M.D Abubakar wanda Suruki ne wurin Mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya fito ya maidawa wadanda ke sukansa a cikin ‘yan kwanakin nan wani martani.

Kamar yadda mu ka samu labari, Jamilu Abubakar ya yi raddi ne ga wadanda ke kiransa “Mijin ‘Diyar Dangote” a maimakon a kira sa da sunansa da na mahaifinsa na yanka.

Har ta kai wasu na cewa ya kamata duk Namiji ya zage da neman na kan-sa domin gudun a rika alakanta shi da Surukunsa. Jamilu ya ba su amsa a shafin sa na sadarwa na Tuwita.

Fitaccen Matashin cikin raha ya ke cewa: “Na ji wasu na cewa in dage da neman na kai na fa! Watakila don ban je na saye wani kadaran da ‘yan gidansu su ka mallaka ba ne.”

KU KARANTA: Kalaman APC da Gwamnati sun jawo mata matsala wajen Iyalin Saraki

Matukin jirgin saman ya cigaba da cewa: “Amma, wata rana za mu kai wurin (Dariya). Gaskiya ya kamata wasu su yi kudi, daga baya kuma su yi amfani da kai domin kara suna.”

A jawabin wannan Bawan Allah ya nuna cewa bai damu domin wani na cin moriyarsa ba, inda ya tike zancensa da nuna cewa mai kyauta ba ya rashi, don haka a iya amfani da shi.

Jama’a sun fara ce-ce-ku-ce a kan Jamil da Iyalinsa ne tun bayan da Mai dakinsa Fatima Dangote ta haihu a kasar waje. Wasu sun fito sun fara surutu cewa Dangote ya cinye sunansa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel