Yanzu Yanzu: Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kashe mutane 6 a Jigawa

Yanzu Yanzu: Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kashe mutane 6 a Jigawa

Rahotanni sun kawo cewa mutane shida sun hallaka sakamakon ruwan sama kamar dab akin kwarya da aka zuwa a jihar Jigawa.

Mutane biyar sun mutu ne a karamar hukumar Kirikissamma yayinda mutum guda ya mutu a wani gini da ya rufto a karamar hukumar Kafin Hausa.

Wata mai juna biyu na daga cikin wadanda suka mutu, bayan gini ya rufto akan su sakamakon ruwan da sama da aka kwashe kwanaki uku ana yi a jihar Jigawa.

An rahoto cewa ruwan ya mayar da kimanin wasu mutane sama da 600 marasa galihu sannan kuma cewa cikowar kogin Hadejia ya taimaka wajen haddasa annobar a yankuna uku na jihar da suka hada da Kirikasamma, Guri da kuma Birnin Kudi.

Mai cikin, Halima Mallam Manu mai shekara 35 da yaranta biyu, Aisha Mallam Manu, yar shekara hudu da kuma Dauda Mallam Manu dan shekara biyu, duk sun rasa ransu bayan dakinsu ya rushe a yayinda suke cikin bacci a kauyen Kuradige da ke karamar hukumar Kirikasamma.

Hakazalika wasu ma’aurata, Musa Wakili dan shekara 4 da matarsa Hauwa Musa mai shekara 35 sun mutu ayan dakinsu ya rufta akansu yayinda Fatsuma Musa mai shekara 20 ta mutu bayan dakinsu na laka ya rushe a kauyen Auno na karamar hukumar Kafin Hausa.

KU KARANTA KUMA: Karkatar da kayan 'yan IDP: Gwamna Zulum ya yi tsinuwa da Qur'ani

Mutane 100 daga karamar hukumar Guri na nan suna hijira a makarantar Firamare da ke garin.

Babban sakataren hukumar bayar da agaji na jihar Jigawa (SEMA), Sani Yusuf Babura ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya bayyana cewa rahoton adadin mutanen da suka mutu wanda ke gabansa hudu ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel