Ba zan taba daina kyautata zato a kan Najeriya ba - Obasanjo

Ba zan taba daina kyautata zato a kan Najeriya ba - Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce babu wani yanayi komai wahala ko mai dadi, da zai sanya ya daina yi wa kasar nan kyakkyawan zato duk da irin munanan kalubale da ta ke fuskanta.

Obasanjo ya yi gargadin cewa, ya zuwa yanzu irin tabarbarewar da harkokin ilimi suka yi a kasar muddin ba a farga ba, wata bakar azaba na iya aukuwa da za ta dulmiyar da kasar ta kuma hana ta kai wa matakin kasaitattun kasashen duniya.

Tsohon shugaban kasar ya kalubalanci dukkanin matakan gwamnati a Najeriya da su mike tsaye wajen bai wa harkokin ilimi muhimmanci, tare da gargadi a kan tunkarar mummunan kalubalen da ya tunkaro kasar na yawaitar adadin mutane.

Gargadin tsohon shugaban kasar ya zo ne a ranar Talata cikin birnin Abeokuta na jihar Ogun, yayin gabatar da jawabai ga wasu matasa da kuma daliban ilimi daga wasu zababbun makarantu na jihar.

Yayin tabbatar da cewa akwai babbar barazana a harkokin ilimi a kasar, Obasanjo ya ce babu dalilin da zai sanya a samu yaran da ba sa zuwa makaranta ba tare da iyaye sun tursasa masu neman ilimi ba.

Tamkar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Obasanjo ya bayyana fargabarsa a kan yadda adadin al'ummar Najeriya ke ci gaba da hauhawa, inda a cewarsa a halin yanzu mutanen kasar sun kusan kai wa miliyan 200.

Ya ce akwai yiwuwar nan da shekaru talatin masu zuwa, adadin mutanen Najeriya zai kai tsakanin miliyan 400 zuwa 415, inda kasar za ta zamto ta uku a duniya ta fuskar yawan mutane bayan kasar Indiya da kuma Sin wadanda ke sahu na gaba.

Shugaban kasa Buhari a ranar Litinin yayin wani taron kwanaki biyu na musamman tare da zababbun ministoci 43, ya bayyana fargabarsa kan yadda adadin al'ummar Najeriya ke ci gaba da karuwa babu kakkautawa, lamarin da ya ce yana matukar razanar da shi.

KARANTA KUMA: An daure wata mata tsawon shekaru 30 da laifin zubar da ciki, an wanketa bayan cin sarka ta shekaru 3 kacal

Ya nemi zababbun ministocinsa da su hada hannu-da-hannu da juna wajen tunkarar duk wani kalubale da ya tunkaro kasar a yanzu. Ya nemi da su tabbatar da hadin kai a tsakanin su domin cimma manufofin gwamnati.

Ya hikaito alkalumman Majalisar Dinkin Duniya UN wadda ta yi hasashen cewa zuwa shekarar 2050, Najeriya za ta kasance kasa ta uku a duniya ta fuskar yawan mutane, wanda ta kiyasta cewa mutanen kasar za su iya kai wa mutum miliyan 411.

Ko shakka babu shugaban kasar ya ce yawan jama'a zai zamto wata babbar damuwa a Najeriya muddin muka ci gaba da zama jiran taimakon kasashen duniya da suka kasaita. Ya nemi sabbin ministoci da su dukufa wajen shimfida tubalin da sai sanya kasar nan kan tafarki na ci gaba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel