Tirkashi: Jarumar Indiya ta wulakanta jarumi Sarki Ali Nuhu

Tirkashi: Jarumar Indiya ta wulakanta jarumi Sarki Ali Nuhu

- Wata jarumar kasar Indiya ta fina-finan Bollywood ta kunyata fitaccen jarumi Ali Nuhu

- Hakan ya biyo bayan kin kula shi da ta yi a shafinta na Instagram bayan ya wallafa hotonta yana yi mata murnar ranar haihuwa

- A ranar 17 ga wannan watan ne jarumar take cika shekaru 31 a duniya, inda kuma take yin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, Ali Nuhu, ya sha kunya bayan jarumar fim ta kasar Indiya ta share shi taki yi masa magana bayan yayi mata magana.

Dabo FM ta bankado cewa fitacciyar jaruma, Shraddha Arya, taki kula jarumi Ali Nuhu ne bayan ya aika mata da sakon taya ta murnar ranar zagayowar haihuwarta.

Jaruma Shraddha Arya, da ta cika shekaru talatin da daya (31) da haihuwa, tana gabatar da bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta a duk ranar 17 ga watan Agusta na kowacce shekara.

KU KARANTA: Adam A Zango ya daura damarar lalata tarbiyyar 'yammata Musulmai na arewa - Datti Assalafiy

Jarumi Ali Nuhu dai ya wallafa sakon ne a ranar 17 ga watan Agustan wannan shekarar a kan shafinsa na Instagram.

Inda har ya zuwa yanzu da muke bada wannan rahoto jarumar ba ta ce masa uffan ba akan hoton nata da ya wallafa.

An gano cewa ya zuwa yanzu jaruma Shraddha Arya ta wallafa sakonnin mutane sittin da daya a shafinta na Instagram wadanda suka taya ta murnar, amma babu Ali Nuhu a ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng