Zaben 2019: Buhari zai roki Kotu ta yi watsi da karar Atiku Abubakar

Zaben 2019: Buhari zai roki Kotu ta yi watsi da karar Atiku Abubakar

Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyarsa ta APC mai mulki a kasar sun roki kotun da ke sauraron karar zaben shugaban kasa na 2019 da ya yi watsi da karar Atiku Abubakar.

A takardun karshen da Muhammadu Buhari da APC za su ka gabatar a Ranar 23 ga Watan Agusta, za su nemi kotu ta yi waje da rokon da Atiku Abubakar da PDP su ke yi na a sauke shugaban kasa daga mulki.

Rahotanni sun zo mana cewa APC da shugaba Buhari za su fadawa kotu cewa tun farko PDP ta tsaida wanda ba ainihin ‘Dan Najeriya ba ne a matsayin ‘dan takarar ta na shugaban kasa a zaben na 2019.

Bayan haka, wanda a ke karar za su kuma nunawa kotu cewa Atiku Abubakar ya gaza ba kotu cikakken hujja da za su gamsar da zargin da ya ke yi na cewa an tafka magudi a zaben na bana da INEC ta shirya.

Shugaba Buhari ya na ganin cewa duk da shaidu fiye da 70 da wasu tarin takardu har 31, 287 da bidiyoyi 48 da Atiku Abubakar ya gabatar, babu abin da ke tabbatar da cewa an murde zaben shugaban kasar.

KU KARANTA: Buhari ya koma bakin aiki bayan gama hutun sallah a gida

Shugaban kasar ya na kuma ganin cewa jam’iyyar PDP da ‘dan takararta, ta yaudari jama’a da sunan cewa hukumar INEC ta kasa yi amfani na’urorin zamani wajen aika sakamakon zaben wannan shekarar.

Buhari da APC za su kare kansu da cewa dokar zabe ba ta san da zaman na’ura wajen hankada sakamakon zabe ba. A cewarsu sashe na 52 da 78 na tsarin zabe ya tanadi fam din EC8 ne domin tattara sakamako.

Haka kuma shugaba Buhari zai yi watsi da korafin da PDP ta ke yi na cewa bai da takardun WAEC. Lauyoyin shugaban kasar za su karyata wannan zargi tare da tabbatar da cewa Buhari ya cika sharudan takara.

A sakamakon zaben da INEC ta bayyana, Buhari ne ya yi galaba da kuri’u fiye da miliyan 15 inda Atiku ya samu 11,262,978. PDP ta dumfari kotu inda ta fadawa Alkalai cewa lalli an murde zaben.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel