Waiwaye: Yadda aka kori Zakzaky daga jami'ar ABU saboda haddasa rikici a shekarar 1979

Waiwaye: Yadda aka kori Zakzaky daga jami'ar ABU saboda haddasa rikici a shekarar 1979

An kori Ibraheem Zakzaky, shugaban kungiyar 'yan uwa Musulmi da ak fi sani da 'Shi'a', daga jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke garin Zaria a shekarar bayan ya jagoranci wata kazamar zanga-zangar yaki da shan giya a makarantar a shekarar 1979.

Zakzaky ya kafa kungiyar IMN tun lokacin da yake karatu a jami'ar ABU domin yada manufa da akidun kungiyar Shi'a, wacce ta fara samun karfi bayan ta kwaci mulkin kasar Iran a shekarar 1979.

Ayatollah Khomeini ne ya kafa daular Shi'a a Iran bayan ya jagoranci zanga-zangar hambarar da mulkin Iran daga a karkashin tsarin sarauta.

Duk da kasancewarsa dalibi mai matukar hazaka da basira, kwamitin ladabtawa na jami'ar ABU ya amince tare da bayar da shawarar a kori Zakzaky tare da shugaban kungiyar dalibai Musulmai a jami'ar, Sani Daura, saboda rawar da suka taka wajen haddasa rikici a makarantar.

Zakzaky bai kammala karatu a sashen ilimin tsimi da tanadi (Economics) ba a hukumance duk da kasancewar yana da sakamako mafi daraja da ake kammala karatun digiri da shi.

DUBA WANNAN: Wata baturiya da mahaifinta sun kashe likitan Najeriya ta hanyar caccaka masa wuka

An samu barkewar rikici a jami'ar ABU yayin da wasu mambobin kungiyar MSS suka dira wurin wani taro da kungiyar dalibai ta shirya domin su nuna rashin amincewarsu da sha da kuma sayar da giya a wurin taron.

A rahoton kwamitin ladabtarwa mai dauke da kwanan watan 2 ga watan Nuwamba, 1979, da sa hannun sakataren kwamitin, S.S Gbinde, mambobin kwamitin sun yi imanin cewa Zakzaky na da hannu wajen ingiza masu zanga-zangar da suka dira wurin taron da kungiyar dalibai ta hada a ranar 20 ga watan Oktoba, 1979.

Ango Abdullahi, mukaddashin shugaban ABU kuma sakataren kwamitin a wancan lokacin, ya bayyana cewa kungiyar MSS ta aika takardar gargadi ga kungiyar dalibai a kan shirya taron.

Zakzaky, wanda ya kasance sakataren kungiyar MSS a zangon karatu na 1977/78 ya shaida wa kwamitin cewa "yana da hannu a cikin shirya zanga-zangar amma babu hannunsa a cikin rikicin da ya barke".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel