Sanata Aisha ta bai wa matasa 385 tallafi a jihar Adamawa

Sanata Aisha ta bai wa matasa 385 tallafi a jihar Adamawa

Mai wakilcin shiyyar Adamawa ta Tsakiya a zauren majalisar dattawa, Sanata Aisha Dahiru Ahmed Binani, a karshen makon da ya gabata ta dauki nauyin shirin tallafawa matasa da kuma mata 385 a kan sana'o'i daban-daban.

Da ta ke gabatar da jawabai a birnin Yola ga matasan da kuma matan da aka tsakuro daga kananan hukumomi bakwai dake karkashin mazabarta, Sanata Aisha ta bayyana koyon sana'ar hannu a matsayin wata matabbaciyar hanya ta yaki da rashin aikin yi a Najeriya.

Ta ce daukar nauyin koyar da sana'ar hannu shi ne abu na farko na inganta jin dadin rayuwar al'ummar mazabarta da za tayi a kan kujerarta. Ta ce koyon sana'ar hannu wata babbar dama ce ta dogaro da kai har na tsawon rayuwa.

Sanata Aisha ta kuma yabawa hukumar samar da ayyukan yi ta Najeriya, NDE, da ta bayar da gudunmuwar hadin gwiwa da kuma goyon baya wajen tabbatar da wannan shiri na tallafawa al'umma a mazabarta.

Ta jaddada cewa, babu wata wariya ta akidar siyasa, jinsi ko kuma ta addini da aka nuna a yayin tsakuro matasan da kuma matan da suka samu wannan babban tallafi na koyon sana'o'in hannu daban-daban da manufa ta samar da abin dogaro da kai.

KARANTA KUMA: Sabbin Dokoki 11 da aka shimfida kan sha'anin aure da zanen suna a jihar Kebbi

Mataimakin gwamnan jihar Crowther Seith, ya yabawa kwazon Sanata Aisha da ta kaddamar da wannan shiri na yakar talauci tare da cewar hakan ya yi daidai da akida da kuma manufofin gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri, na tabbatar da matasa sun kaurace zaman kashe wando.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel