Yar wasar kudu ta koka akan kamun daraktan Kannywood Sanusi Oscar

Yar wasar kudu ta koka akan kamun daraktan Kannywood Sanusi Oscar

Yar wasar kudu, Kate Henshaw, ta je shafinta na zumunta inda ta nemi ayi wa daraktan dandalin shirya fina-finan Hausa, Sanusi Oscar adalci, wanda aka tura gidan yari kwanan nan kan sakin wani bidiyo a Youtube ba tare da izinin hukumar tantance fina-finai na Kano ba.

A cewar rahotanni, Sanusi yayi kokarin kare kansa a kotu, inda ya bayyana cewa shi daraktan bidiyon ne kawai sannan cewa baya da hannu wajen rarraba bidiyon.

Sai dai kuma wasu rade-radi da ke yawo sun bayyana cewa an kama shi ne saboda kin goyon bayan gwamnati mai mulki.

Kate Henshaw wacce ta je shafinta na zumunta ta nema wa daraktan adalci, ta rubuta: “Wannan shine Sanusi Oscar, daraktan fina-finan Hausa. Hukumar tantance fina-finai na Kano karkashin jagorancin Ismaila Afakallah sun kama shi, sun kais hi kotu kai tsaye sannan alkalin ya ki bayar da belinsa sannan aka tura Oscar kai tsaye zuwa gidan yari.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ma’aikatan jami’o’in Najeriya sun fara yajin aiki

“Laifinsa? A watan da ya gabata, ya saki wani bidiyon waka a YouTube ba tare da izini ba (shin ana bukatar hukumar tantance fina-finai a nan?) sannan shekaru hudu da suka gabata ya saki wani bidiyon waka a kasuwa ba tare da satifiket daga hukumar tantance fina-finai ba...

“Sanusi ya fada ma kotu, shi daraktan bidiyon ne kawai, ai kasance mawaki, furodusa ko mai rarraba bidiyon ba. Bayani da ke iso mani ya nuna cewa an kama shi ne saboda ya ki marawa gwamnatin Ganduje mai mulki baya. Wannan ba daidai bane sannan abun Allah wadai ne. Rashin yi wa wani adalci daidai yake da rashin yi wa kowa adalci.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel