Kannywood: Babu ruwan Ali Nuhu da kamun da aka yi wa darakta Sanusi Oscar - Na hannun daman Sarki Ali
Kamar yadda muka sani, sabon rikici ya kunno kai a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, tun bayan billowar labarin kamu da aka yi wa daya daga cikin daraktocin masana'atar mai suna Sanusi Oscar.
Sai dai mutane da dama sun nuna yatsa ga babban jarumi kuma darakta, Ali Nuhu wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood, inda suke zarginsa da hannu a cikin kamun Sanusi saboda banbancin akidar siyasa.
Hakan ne ya sanya mai kula da ragamar dandalin masoyan jarumi Ali Nuhu ya fito yayi wasu bayanai tare da wanke Ubangidan nasa daga zargin da ake masa.
A wani rubutu da ya wallafa a shafin sadarwa ta Instagram yace: "Tun daren jiya bayan ganin wasu rubuce-rubuce na wasu mutane da kuma wani bidiyo na wata mata. Nake son yin rubutu domin yin martani ko Kuma nace nisanta Maigidanmu daga sharri da kazafi da ake yi Masa. Biyo bayan wata Dambarwa dake faruwa tsakanin hukumar tace finafinai da kuma wani Darakta.
"Da farko dai Ina so jama'a su san cewa Ali Nuhu a Kannywood matsayinsa shine Jarumi, Darakta, Mai shiryawa da Kuma wasu bangarori kamar Rubuta labari da sauransu. Baya ga haka shi mabiyi ne a cikin dukkan wasu kungiyoyi na Kannywood. Ma'ana baya cikin shugabanci. Balantana Kuma Uwa Uba Hukumar tace finafinai. Wacce ba shi da katabus a cikinta.
"Sannan kuma a duk cikin Kannywood babu wani mutum da siyasa ta shiga tsakanin kyakkyawar mu'amalarsu da Ali Nuhu. Misali, dukkanin manyan aminansa na Kannywood basa ra'ayi daya da shi a siyasa (Sani Danja, Yakubu Muhammad, Abba El-Mustapha da sauransu). Shin kun taba jin sabani tsakaninsu?
"Ni din nan da nake tafiyar da wannan shafin duk Wanda ya sanni a ko Ina a duniya yasan cewa ni DAN KWANKWASIYYA ne na gaske. Tun daga 1999 nake cikinta Kuma nake gwagwarmaya a cikinta. Amma Ali Nuhu bai taba nuna min canji a fuska ko a mu'amala ba. Sai dai ma mu tattauna akan akidunmu.
KU KARANTA KUMA: Tirkashi: Sabon rikici ya barke tsakanin Muneerat Abdulsalam da mawaki Misbahu M Ahmad
"Ina kira ga jama'a 'yan fim da Wanda ba dan fim ba. A duk lokacin da wani abu ya faru, ko Kuma kaji wani batu to ka tuntuba ka tabbatar da yadda lamari yake kafin ka yi magana akai. Sannan Ina so jama'a su san cewa idan akwai rikici tsakanin wancan Darakta da wani Wanda ya sa aka kama shi kamar yacce ake fada, to ba Ali Nuhu bane.
"Muna fata Allah ya tsare mutuncinmu, ya tsare imaninmu, ya Kuma habbaka tunaninmu."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng