Gaskiyar dalilin da ya sa APC ta dakatar da Abdulmumini Jibrin

Gaskiyar dalilin da ya sa APC ta dakatar da Abdulmumini Jibrin

Ba a bukatar ambatan sunan Abdulmumini Jibrin, mamba mai wakiltan Kiru/Bebeji na jihar Kano a majalisar wakilai sau biyu, idan har aka zo kan batun rigima. Kwanan nan ne dai dan majalisar ya sake afkawa cikin wani sabon rikicin siyasa kan zargin yin ayyukan da suka saba ma jam’iyya a mazabarsa.

Idan ba don kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila yace babu wata a kasa ba, da ba zai zamo laifi ba idan aka ce an hana Jibrin mukamin shugabantar wani kwamiti a majalisar wakilai ne, duk a cikin kokarin hukunta shi kan zargin da ake masa.

Gbajabiamila yace Jibrin ne ya nuna baya muradin kowani mukami na shugabanci a majalisa ta tara. Hasashe sun nuna cewa dan majalisar daga Kano na tsimayin babban mukami daga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a nan gaba kadan.

A lokacin majalisa ta takwas, an bai wa Jibrin wanda ya taka rawar gani wajen ganin Yakubu Dogara wanda ke APC a wancan lokacin ya zama kakakin majalisar wakilai mukamin Shugaban kwamitin kasafin kudi.

Sai dai kuma an sauke shi daga shugabancin kwamitin tare da dakatar dashi daga majalisar akan rikicin aragizon kasafin kudi, lamarin da ya dauki dogon lokaci ana fama a majalisar dokokin tarayyar.

A lokacin da ya dawo, ya natsu ya kuma fara shirye-shiryen zaben 2019 na kasa, ya hada kai da kungiyar da ta tsayar da Gbajabiamila (APC Lagos) a matsayin kakakin majalisar wakilai.

Hakika, ya kasance Babban Darekta na kungiyar yakin neman zaben Gbajabiamila, yawancin sun dauka za a sake sanya shi a wani gagarumin kwamiti. Haka zalika hakan bai faru ba; maimakon haka, lamarin samun babban mukami daga Gwamnatin Tarayya ya kunno kai.

A wannan yanayin ne lamarin dakatar da shi yazo daga Kano, kuma hakan ya sanya tsoron cewa ana iya sallamar shi daga jam’iyya mai mulki.

An zargi Jibrin da gudanar da ayyukan da suka saba ma jam’iyyar APC, a lokacin zaben na kasa da ya gabata, musamman a lokacin zabbukan gwamna da na yan majalisar dokokin jiha.

An zargi dan majalisar da gudanar da yakin kayar da dan takaran APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ke takarrn gwamna karo na biyu a lokacin zaben. Ya kuma yi aiki don ganin faduwar Alhaji Usaini Danbirni Jibril wanda ya kasance dan takara a majalisan jihar.

Sauran laifuffukan da Jibrin ya aikata sun hada da cin zarafin Shugabancin APC a Kano a lokacin wani shiri na radiyo wanda shine ya dauki nauyin shirin, karkatar da alawus a lokacin zaben 2019 da kuma shirya kansiloli don yin zanga-zangar neman tsige shugaban karamar hukumar Bebeji mai mulki, Alhaji Ali Namadi.

Sakamakon saba ma ayyukan jam’iyyar ne yayi sanadiyar nasaranr jam’iyyar adawa ta PDP a karamar hukumar Bebeji.

An tattaro cewa lokacin da aka gabatar da lamarin a gaban kwamitin APC a Bebeji, sai aka kafa kwamitin mutum bakwai karkashin jagorancin Alhaji Musa Salihu Bebeji domin su binciki lamarin.

Sai dai kuma da kwamitin ta gayyaci Jibrin domin ya gurfana a gabanta, sai yayi watsi da gayyatar ba tare da kowani dalili ba.

KU KARANTA KUMA: Ali ya ga Ali: Yadda ziyarar Shugaban Guinea ta hada Ganduje da Sarki Sanusi har sau 6

Sannan sakamakon haka, sai kwamitin ta tattara rahotonta sannan ta gabatar dashi ga kwamitin kamar yadda ya umurta.

Daga nan sai shugabannin APC a Bebeji suka kira taron manema labarai a ranar 30 ga watan Yuli, inda ta aiwatar da shawarwarin da kwamitin mutum bakwai ya bata.

Sai dai duk wani kokari da aka yi domin jin ta bakin Jbrin kan lamarin ya ci tura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel