Wasu Sojojin Najeriya sun sake kashe mutane 3 a Jihar Legas

Wasu Sojojin Najeriya sun sake kashe mutane 3 a Jihar Legas

Kusan mako guda ke da wuya da sojoji su ka kashe wasu ‘yan sanda ne mu ka sake samun labarin cewa Dakarun sojojin kasar sun kuma hallaka wasu mutane uku a Kudancin Najeriya.

Wasu daga cikin Dakarun Bataliyar sojoji ta 81 sun aika wasu Mazauna Garin Isheri Olofin lahira ne a kwanan nan. Wannan Kauye ya na kan iyaka ne tsakanin jihar Legas da kuma jihar Ogun.

Kamar yadda mu ka samu labari, wannan abin takaici ya faru ne a Ranar Litinin a lokacin da a ka shirya wani biki a Isheri. Dama can akwai kullaliya tsakanin wani mai suna Tiri da ‘yan garin.

Yayin da Sojoji su ke kokarin kutsawa da wannan mutumi zuwa cikin wata kasuwar dabbobi ne rigima ta kaure inda jama’a su ka yi kokarin hana su wucewa, nan take jami’an su ka buda wuta.

Kafin a motsa wadannan Sojoji su ka kashe mutane biyu yayin da guda kuma ya samu rauni a sakamakon harbin da sojoji su ka yi. A nan ne a ka ruga da wanda ya samu rauni zuwa asibiti.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun kashe wani Malamin addini a kasar China

Majiyar ta bayyana cewa Sojojin sun dare babur sun tsere bayan ganin abin da ya faru. Mutanen da ke yankin sun yi kokarin bin sojojin inda su ka damke wani su ka yi masa rotsen duwatsu.

Bayan sojojin sun kai ‘danuwansa da a ka yi wa ature ne su ka hadu da wanda su ka yi wa rauni. A nan ne su ka yi amfani da makami su ka karasa kashe shi har lahira kamar yadda mu ka ji labari.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu ‘yan sanda na jihar su na neman wadannan Sojoji inda Rundunar sojojin yankin su ka karyata cewa akwai hannun Jami’ansu a cikin wannan kisa.

Jama'an garin sun yi kokarin amfani da wannan ranar biki ne domin goge raini kafin abin ya cabe. An gane wadanda su ka mutu ba tare da sun shura ba a matsayin Damilare Adelani da Tayese.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel