Suhaila El-Zakzaky ta bayyana halin da mahaifanta suka shiga a Indiya

Suhaila El-Zakzaky ta bayyana halin da mahaifanta suka shiga a Indiya

Rahotanni daga kasar Indiya sun nuna cewa an samu matsala kan likitocin da za su duba jagoran kungiyar Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-zakzaky da mai dakinsa bayan da suka isa kasar domin yin magani.

Daya daga cikin 'ya'yansa mai suna Suhaila ta bayyana cewa: "An ce an tsare su ne a asibitin, kuma sunce ko daga daki zuwa daki a cikin asibitin basa iya motsawa, an hana su motsi. Sannan kuma an ganin likitocinsu wanda tun asali wadannan likitocin nasu ne suka zabi daman su je wannan asibitin."

Suhaila ta kara da cewa: “Bisa ga shawarwarin likitocinsu suka ce su je wannan asibitin, da tunanin cewar koda sun je asibitin, dama lamarin karatun likitanci ba wai dole-dole sai likitanka bane zai duba ka akan komai ba, amma ko babu komai kana iya zuwa bisa ga shawarar shi wannan likitan.

“A sanadiyar cewa sun yi magana da nasu likitocin sai suka bayar da shawarar zuwa wannan asibitin, cewa shi yafi dacewa, toh kuma sai gashi bayan sun je din yanzu hukumar asibitin sun ce lallai sai dais u ne za su yanke hukunci akan likitan da zai duba su, wanda kuma ko a Najeriya da suke rike a hannun DSS, an yarda da suna iya zabar likitan da zai duba su, domin a tsare suke bayan sojan Najeriya ya kai masu hari."

KU KARANTA KUMA: Mutanen da ke kashe bayin Allah sannan suna ihun Allahu Akbar makaryata ne - Buhari

Da aka tambaye ta kan ko har yanzu ba a fara duba mahaifin nata ba tace: “har yanzu babu wani magani da aka fara yi mai.”

Wasu majiyoyi sun ce gwamnatin kasar ta Indiya ta ba malamin wani wa'adi na ya koma Najeriya idan bai amince da likitocin da aka ba shi ba, sai dai Suhaila ta ce har yanzu bai yanke shawara kan hakan ba.

Sai dai kawo yanzu hukumomin asibitin, wanda shi Zakzaky ne da kansa ya zabi zuwa can, ba su ce komai ba kan wadannan zarge-zarge.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel