Mutanen da ke kashe bayin Allah sannan suna ihun Allahu Akbar makaryata ne - Buhari

Mutanen da ke kashe bayin Allah sannan suna ihun Allahu Akbar makaryata ne - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yan ta’addan da ke yawo suna kashe bayin Allah da bama-bamai da wukake yayinda suke ihun ‘Allahu Akbar’ ba su san Allah ba sannan kuma karya suke yi.

Shugaba Buhari yakuma bayyana cewa dukkanin mutanen da ke aikata irin wannan mugun aiki karya suke yi saboda “addinin Islama bai ba kowani mutum ikon kashe wani batare da bin tsarin kotu ba."

Shugaba Buhari yayi jawabin ne a lokacin da ya ziyarci sansanin yan gudun hijira a kananan hukumomi takwas na jihar Katsina wadanda suka hada da: Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Jibiya, Sabuwa, Faskari da kuma Dandume.

Yace ya ziyarce su ne domin yi masu jaje akan kashe-kashen da yan taáddan Boko Haram suka yi da sunan addini.

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani ya goyi bayan umurnin da Buhari ya bai wa CBN kan hana shigo da abinci

A cewar Shugaban kasar, “Dukkanin mutanen da ayyukansu shine kashe mutane da kuma fadin ‘Allahu Akbar’ toh makaryata ne saboda Allah ba azzalumi bane. Ba zai yiwu ka dauki bindiga ko bam, ko wuka ko takobi ka je ka kashe wani sannan kace ‘Allahu Akbar’ ba. Hakan na nufin baka yi imani da Allah ba ko kuma baka san me kake fadi ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel