Tarihin attajirin mai garkuwa da mutanen da ya haddasa rikici tsakanin 'yan sanda da sojoji
Batun rikicin da ya faru tsakanin dakarun soji da jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Taraba na daga cikin manyan labaran da suka mamaye kafafen yada labarai a cikin 'yan kwanakin nan.
Ana zargin cewa akwai wata kitimurmura tsakanin wani attajirin mai garkuwa da mutane a jihar Taraba da wasu dakarun soji da suka kubutar da shi daga hannun jami'an 'yan sanda tare da kashe uku daga cikinsu.
Mutumin da ake zargi zama silar rikicin sunansa Hassan Bala, wanda aka fi kira da tsokanar 'why do you mean?' wanda wasu suka mayar da shi 'Wadume' saboda basu san yadda ake furta sunan da harshen turanci ba.
Ya fara sana'ar sayar da kifi, daga baya ya koma sana'ar fenti sannan yana taba harkokin siyasa. Ya yi aure tare da haifar yara barkatai kuma ya kasance mai taimakon jama'a da dukiyarsa.
Ana tunanin jama'a na zuzuta arzikinsa ne saboda kyautarsa da kuma kashe kudi ba tare da jin zafin fitarsu ba.
Ana zargin cewa ya samu arzikinsa ne ta hanyar garkuwa da mutane.
Mahaifinsa mutumin asalin jihar Katsina ne wanda ya yi hijira zuwa Ibi a jihar Taraba inda har ya auri mahaifiyar 'Wadume' wacce 'yar asalin kabilar Tiv ce daga karamar hukumar Ukam a jihar Taraba.
An haife shi a karamar hukumar Ibi inda ya halarci makarantar firamare da sakandire. Abokansa sun ce bashi da kokari lokacin da suke makaranta tare, lamarin da yasa bai cigaba da karatu ba bayan kammala sakandire.
Bayan ya kammala karatun sakandire a shekarar 2004, Hassan ya shiga sana'ar suyar kifi kafin daga bisani ya fada cikin siyasa inda ya nemi takarar majalisar jiha a jam'iyyar YPP a shekarar 2019.
Jami'an rundunar 'yan sanda sun gano cewa Hassan shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane ne bayan an kama daya daga cikin yaransa mai suna 'Kwarba' a Jalingo bisa zarginsa da hannu a garkuwa da wani babban sakatare a gwamnatin jihar Taraba.
Kwarba ne ya sanar da jami'an 'yan sanda cewa Hassan Wadume ne shugabansu.
Kwarba ya bawa jami'an 'yan sanda ta hanyar cigaba da yin waya da Wadume duk da yana tsare. A cikin hirarsu ne ya fada wa Kwarba cewa zai shigo Ibi da Sallah.
Kwarba ya nuna wa jami'an 'yan sanda Wadume yayin da yake zaune a wani wurin shan shayi bayan ya shigo garin Ibi.
Jami'an 'yan sanda sun zo cikin farin kaya tare da yi masa wayon cewa sun zo sayar masa da wata mota, bayan ya shiga motar domin duba ta sai jami'an 'yan sanda suka saka masa ankwa a hannu da kafa suka tafi da shi.
Amma bayan jami'an 'yan sanda sun biyo ta cikin gari domin fita da shi sai ya leko ta tagar mota yana ihun cewa an sace shi, lamarin da yasa yaransa suka hada jama'a tare da hawa babura su bi motar a yayin da take barin garin Ibi.
A wannan yanayi ne ake tunanin wasu sun sanar da wani Soja mai alaka da Wadume cewa an sace shi, shi kuma sojan ya debo sojoji suka biyo motar 'yan sanda kuma bayan sun cimmasu suka tsayar da su suka harbe su sannan kuma suka saki Wadume.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa Wadume ya koma cikin garin Ibi tare da yin murnar kubutarsa tare da yaransa kafin daga bisani ya sulale ya bar gari ba tare da sanin kowa ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng