Sanata Ahmed Lawan ya dawo daga aikin Hajji

Sanata Ahmed Lawan ya dawo daga aikin Hajji

Biyo bayan kaddamar da sabbin kwamitoci da aka gudanar a baya-bayan nan, shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya ce majalisar Tarayya ta shirya tsaf domin sauke nauyin da rataya a wuyanta wajen yiwa 'yan Najeriya aiki tukuru.

Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne ga manema labarai a harabar filin jirgin saman kasa-da-kasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja, yayin dawowa daga kasar Saudiyya inda ya gudanar da aikin hajji a bana.

Yayin yi wa Sanata Ahmed Lawan lale maraba na dawo daga aikin Hajji
Yayin yi wa Sanata Ahmed Lawan lale maraba na dawo daga aikin Hajji
Asali: Twitter

Sanata Ahmed Lawan yayin zantawa da manema labarai bayan dawo daga aikin Hajji
Sanata Ahmed Lawan yayin zantawa da manema labarai bayan dawo daga aikin Hajji
Asali: Twitter

Sanata Ahmed Lawan yayin barin filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe bayan dawo wa daga aikin Hajji
Sanata Ahmed Lawan yayin barin filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe bayan dawo wa daga aikin Hajji
Asali: Twitter

Sanata Ahmed Lawan yayin barin filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe cikin tawagar sanatoci da hadimai bayan dawowa daga aikin Hajji
Sanata Ahmed Lawan yayin barin filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe cikin tawagar sanatoci da hadimai bayan dawowa daga aikin Hajji
Asali: Twitter

Sanata Lawan ya dawo Najeriya da duku-dukun ranar Alhamis, inda Sanata Jibrin Barau, Sanata Michael Opeyemi Bamidele da kuma shugaban ma'aikatansa, Muhammad Karage suka tarbe sa kamar yadda mai magana da yawunsa Ola Awoniyi ya bayar da shaida.

KARANTA KUMA: Dan sanda ya harbe kansa a Amurka

Ana iya tuna cewa a ranar Litinin 5 ga watan Agustan 2019, shugaban majalisar ya yi baluguro zuwa kasar Saudiya domin sauke farali na aikin Hajji a bana cikin tawagar wasu Sanatoci da suka hadar da Sahabi Alhaji Ya'u, Teslim Folarin, Bello Mandiya, Ajibola Bashiru da kuma Sani Musa.

A yayin rokon Mai Duka da ya jibinci lamarin kasar nan wajen kawar da duk wani kalubale da take fuskanta musamman rashin tsaro, shugaban majalisar ya kuma yiwa Allah godiya da ya bashi damar kasancewa cikin 'yan Najeriya fiye da 60,000 da suka sauke farali yayin aikin hajji na bana.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel