Babbar Sallah: Manyan Sarakunan Arewa sun aika da muhimman sakonni

Babbar Sallah: Manyan Sarakunan Arewa sun aika da muhimman sakonni

A ranar Lahadi, 11 ga watan Agusta, wanda ya yi daidai da 10 ga watan Zulhijja ne aka gudanar da shagulgulan babbar Sallah a Najeriya, kuma kamar yadda aka saba, shuwagabbanin gargajiya da Sarakuna sun gabatar da jawabai daban daban bayan idar da Sallar Idi.

Da fari dai, mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris ya yi kira ga shuwagabanni a matsakin jaha da gwamnatin tarayya dasu sama ma jama’a sauki daga cikin wannan kangin rayuwa da suka fada.

KU KARANTA: An karrama gwamnan Kaduna da babbar Sarauta a yayin bikin babbar Sallah

Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar da jawabinsa na barka da Sallah a fadarsa dake birnin Zazzau, inda ya nemi gwamnatoci a dukkanin matakai dasu jajirce wajen kula da walwalar yan Najeriya.

Shima a nasa jawabin, Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo ya gargadi tsofaffin shuwagabanni da shuwagabanni masu ci dasu kauce ma furta munanan kalaman da ka iya tarwatsa Najeriya. Sarkin ya koka kan yadda wasu shuwagabanni ke magana ba tare da lissafi ba.

“Sakonnin kiyayyasun yi yawa a wannan lokaci, musamman daga bakunan maluma da shuwagabannin al’umma, don haka dole da mu dakatar da wannan matsala kafin mu zama kamar kasashen Rwanda da Burundi.” Inji shi.

Shi kuwa mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq addu’a ya yi Allah yak are shugaban kasa Muhammadu Buhari daga makiyansa, sa’annan ya kara da tabbatar ma Buharin cewa sai ya ga bayan makiyansa da ikon Allah.

Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya jinjina ma gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje bisa kokarin da gwamnatinsa ke yi na tabbatar da tsaro a duk fadin Jihar Kano, sa’annan ya yi kira ga gwamnan daya samar da isasshen takin-zamani da sauran abubuwan da za su inganta harkokin noma ga manoman Kano.

Da yake nasa jawabin, sha kurukundum, jikan Danfodiyo, kuma shugaban Sarakunan Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar ya nemi yan Najeriya dasu kasance masi jin tsoron Allah, tare da kokarin zaman lafiya da junansu a yayin bikin Sallah da ma bayan Sallah.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel