Allah ya sa ka ba Makiya kunya – Sarki Faruk ya yi wa Buhari addu’a

Allah ya sa ka ba Makiya kunya – Sarki Faruk ya yi wa Buhari addu’a

- Sarkin Daura ya yi wa Muhammadu Buhari wajen bikin babbar sallah

- Basaraken ya yi addu’a ga Ubangiji ya cigaba da kare Shugaban kasar

Mai martaba Sarkin Daura, Umar Faruq Umar, ya roki Ubangiji ya cigaba da kare shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sarkin ya yi wa shugaban kasar addu’a ne a Ranar da Musulman Duniya ke bikin Sallah.

Mun ji cewa Sarkin ya yi wannan addu’a ne a lokacin da a ka yi sallar idi a filin Kofar Arewa da ke cikin Garin Daura a jihar Katsina. An yi sallar ne a da safiyar Ranar Lahadi, 11 ga Watan Agusta, 2019.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi sallah a Mahaifarsa tare da Alpha Conde

Alhaji Umar Faruq Umar ya ke cewa babu magautan da su ka ga bayan shugaban kasa Buhari.

Mai martaban ya ke fadawa Muhammadu Buhari cewa:

“Mu na alfahari da kai; mu na alfahari kuma da gwamnati ka, za mu cigaba da yi maka addu’a.”

Sarki Faruk ya cigaba da cewa: “Za ka (Shugaba Buhari) cigaba da ba maradanka kunya.”

Shugaban na Najeriya ya na tare da Takwaransa na kasar Guinea watau shugaba Alpha Conde a Mahaifar ta sa ta Daura. Shugaban Najeriya Buhari ya saba yin sallah ne a Garin Daura muddin ya na kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel