Yanzu-yanzu: Gwamnan Zamfara ya nada sabon sarkin Maru

Yanzu-yanzu: Gwamnan Zamfara ya nada sabon sarkin Maru

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawallen Muradun, ya nada Abubakar Maigari, matsayin sabon sarkin Maru.

Mataimakin gwamnan jihar, Mahadi Gusau, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 10 ga watan Agusta, 2019.

Nadinsa ya biyo bayan kwance rawanin tsohon sarkin Maru, Abubakar Cika, wanda kwamitin bincike ta tabbatar da cewa yanada hannu cikin harkokin yan bindigan da suka addabi jihar Zamfara.

Hakazalika, gwamnan ya tsige hakimin Kanoma, Lawal Ahmad, kan laifin hada kai da yan bindiga.

An fara zargin Abubakar Cika da Lawal Ahmad a watan Yuli ne inda yan bindiga suka kai mumunan hari garin Kanoma inda akalla mutane 30 suka rasa rayukansu.

A kalla mutane 11 sun mutu a ranar Asabar yayin wani mummunan hatsarin mota da ya faru tsakanin wata mota kirar Sharon da Trela a garin Damba da ke kilomita hudu kudancin Gusau babban birnin jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: Matasa sun hallaka dan sandan da ya harbe mai juna biyu bisa ga kuskure

Mazauna garin sun shaidawa Daily Trust cewa Sharon din mai dauke da mutane 11 daga Abuja a hanyarta zuwa kauyen Jangeru a karamar hukumar Shinkafi na jihar tayi karo ne da wata trela da ke fitowa daga Gusau

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel