Richard McKinney: Sojan da ya shirya sanya bam a Masallaci ya karbi kalmar Shahada yayin da ya shiga Masallacin da mugun nufi
- Wani sojan ruwa da ya yiwa addinin Musulunci tsana ta karshe ya Musulunta cikin ikon Allah bayan yaje masallacin da mugun nufi
- Sojan ya gama shirin sanya bam a cikin Masallacin da zai iya kashe sama da mutane dari biyu, amma sai Allah ya canja ra'ayinsa
- 'Yar gidan sojan ce ta nuna bata son abinda mahaifin nata zai yi shine dalilin da yasa ya canja ra'ayi
Allah yana shiryar da wanda ya ga dama a lokacin da ya so. Ko da makiyanshi idan ya so sai ya mayar dasu masoyanshi cikin lokaci kankani. Tarihi ya kawo labarai masu yawan gaske na mutanen da ba sa kaunar Musulunci amma da sun zauna da Musulmi sai soyayyar addinin ta shiga zuciyarsu, inda har take kai su ga shiga addinin na Musulunci.
Wannan labarin wani sojan ruwane wanda ya tsani addinin Musulunci matuka, inda har yayi shirin zuwa ya sanya bam a masallaci, amma cikin ikon Allah sai ya koma addinin Islama.
Sojan wanda da yake da suna Richard Mac McKinney, yanzu ya koma Omar Saaed Ibn Mac, shine shugaban cibiyar addinin Islama na Moncie dake jihar Indiana, cikin kasar Amurka. Komawarshi addinin Musulunci daban labarin yake da na sauran mutane, saboda na shi labarin ya fara da tsanar addinin Musulunci.
Richard tsohon sojan ruwane wanda yayi aiki da kasar Amurka, kuma yayi aiki a kasashen Musulmai kala daban-daban a tsawon rayuwarshi. Ya kashe Musulmai da yawan gaske lokacin yake yaki a kasashen Musulmi, kuma yana rubuta sunan duk wanda ya kashe a kirjinshi domin kirga yawansu.
Bayan kammala yakin su kuma sai ya shiga damuwa matuka, inda har ya koma shan giya, kuma yaji tsanar Musulmai ta kara shiga rayuwarshi, ta inda yaji yana so ya karar da dukkanin Musulman duniya.
KU KARANTA: Wata tsohuwa 'yar shekara 95 da ta fara shan tabar wiwi tun tana 'yar shekara 10 a duniya
Wana tsana ta kai matsayin da yaje ya fara shirin zuwa ya sanya bam a cikin wata cibiyar addinin Musulunci dake garin shi na Moncie. Nan take ya fara shirin hada bam nashi, wanda zai iya kashe sama da Musulmai dari biyu (200+). Hakan kuma bai sa yayi tunanin wannan abu zai iya sawa yayi zaman gidan yari ba saboda idon shi ya rufe.
Amma kana taka Allah na tashi. Ya taba yiwa 'yarshi maganar irin tsanar da yake yiwa addinin Musulunci sai yaga ranta ya baci. Duk da dai cewa ya tsani addinin amma baya so ran 'yarshi ya baci, kuma ya tabbata idan ya aikata wannan abu da ya shirya 'yarshi ba za ta taba yafe mishi ba.
Hakan ya sa ya fara zuwa Masallatai yana yin tambayoyi, mutanen Masallatan suka dinga karramashi har suka bashi Qur'an ya tafi dashi gida ya karanta. Abin da ya gani a Masallatan bai yi kama da abinda yake kallon Musulmi dashi ba.
Cikin abinda bai fi sati takwas ba da kai ziyara Masallatan ya karbi kalmar shahada, kuma ya shiga addinin Musulunci, daga baya har aka bashi shugaban daya daga cikin manyan Masallatan garin. Ya canja sunanshi zuwa Omar Saeed Ibn Mac.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng