To fah: Wani dan luwadi ya fito takarar shugaban kasa a Tunusiya

To fah: Wani dan luwadi ya fito takarar shugaban kasa a Tunusiya

- Dan luwadi zai bar tarihi a duniya yayin da ya fito takarar shugaban kasa a kasar Tunusiya

- An bayyana cewa dan luwadin shine mutum na farko mai irin wannan akidar da ya fara fitowa takara a yankin gabas ta tsakiya

- An taba daure dan luwadin a gidan yari na tsawon wata uku saboda yayi lalata da wani dalibi dan shekara 17

Wani dan luwadi mai suna Mounir Baatour, ya fito takarar shugaban kasa a kasar Tunusiya, inda zai zamo mutum na farko a yankin gabas ta tsakiya dan luwadi da zai rike irin wannan mukami.

Fitowar Baatours takara shine na farko a cikin mutane irin shi, inda ake ganin zai bar tarihi sosai a duniya. Baatour wanda yake jigo a jam'iyyar Liberal Party sannan kuma lauya a kotun Cassation, ya bayyana kanshi a matsayin wanda yake kare hakkin auren jinsi.

Bayan ya bayyana ra'ayinshi na fitowa takara, kungiyoyi da yawa sun rubuta sammaci inda suka bayyana cewa fitowa takarar shi zai zame musu matsala ga al'ummarsu.

KU KARANTA: Allah wadan naka ya lalace: 'Yar gidan Charley Boy ta wallafa hotunan da ta dauka da abokiyar madigonta

Baatour yayi zaman gidan yari na tsawon watanni uku a shekarar 2013, inda ake zargin shi da lalata da wani dalibi dan shekara 17 a duniya.

Dan mutum ya taba aikata laifi ba zai hana shi fitowa takarar siyasa ba a kasar Tunusiya.

"Dan na zama dan luwadi ba yana nufin ina da matsala bane, na fito takara ne kamar yadda kowa yake fitowa. Ina da kwarewa a bangaren tattalin arziki, al'ada, ilimi da dai sauran abubuwan da suka shafi mutanen Tunusiya," in ji Baatour.

Ana sa ran 'yan takara a kasar Tunusiya su kai takardun neman takararsu daga nan zuwa Juma'a domin yin takara a ranar 15 ga watan Satumbar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel