Babbar Sallah: Hotunan irin tarbar ban girma da aka yi wa Buhari a Daura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar babban birnin tarayya Abuja domin zuwa garin Daura da ke Katsina.
Shugaban kasar zai yi hutun Eid-el-Kabi wato babbar sallah a garin na Daura.
Da isarsa jihar Katsina, Gwamna Aminu Bello Masari da wasu jiga-jigan 'yan siyasar jihar Katsina sun tarbi shugaban kasar da dansa Yusuf Buhari.
Daga nan ne shugaban kasar ya kama hanya zuwa mahaifarsa wato Daura inda gidansa ya ke.
DUBA WANNAN: Abun kunya: Dan majalisar PDP ya yi wa wata mata zigidir a bainar jama'a
Bayan isarsa Daura, Shugaban kasar ya gana da Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar da wasu sauran manyan mutane da masu sarauta a garin da suka zo masa maraba da zuwa.
Ana sa ran za ayi bikin babban sallar ne a ranar Lahadi. A yayin da ya ke Daura, shugaban kasar zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar Katsina ta kammala.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng