Labarin wani mutumi da ya yi shekara 40 ba tare da yayi aski ba

Labarin wani mutumi da ya yi shekara 40 ba tare da yayi aski ba

- Wani mutumi dan kasar Indiya ya shafe shekara arba'in ba tare da yayi aski ba

- Mutumin mai suna Sakal ya bayyana cewa yayi hakan ne saboda wasu dalilai da yake dasu

- Mutanen yankin su na karrama shi sosai, inda da yawa suke zuwa wajensa neman maganin gargajiya

Wani tsohon mutumi mai shekaru 63 a duniya, mai suna Sakal Deb Tuddu dan kasar Indiya ya bayyana cewa ya shafe sama da shekara arba'in bai yi aski ba, sannan kuma bai wanke kansa ba.

Wannan dalili ne yasa gashin nasa yayi tsawo sosai, inda a lokuta da dama yake daure gashin ya mayar dashi kamar rawani, a haka yake yawo zuwa duk inda yake so a gari.

Sakal wanda aka haifeshi a kauyen Mandada dake jihar Bihar a yankin gabashin kasar ta Indiya, ya ce, ya ki yin aski ne tun yana dan shekara 22 saboda wasu dalilai.

Ya bayyana cewa akwai ranar da ya tashi da safe kawai sai ya tarar da gashin kansa ya daddaure saboda rashin aski da kuma wankewa.

KU KARANTA: APC na tsaka mai wuya: Wasu na hannun daman shugaba Buhari sun sauya sheka tare da sama da mutane 6,000 daga jam'iyyar APC zuwa PDP a jihar Zamfara

Ya ce ya yanke hukuncin daina aski ne, yayin da yaga kamar wata karamace abin bautarsa na Hindu wanda suke kira da 'Shiba' yayi masa.

Yanzu da gashin yayi tsawo, sai ya koma nade shi tamkar rawani, a lokuta da dama idan zai fita daga gida yawo yakan yi amfani da farin rawani sai ya rufeta saboda dattin da tayi.

Tun lokacin da Sakal ya daina aski, mutanen yankin suka fara yi masa lakabi da 'Mahatma Ji' musamman mutanen Mandada a matsayin suna na girmamawa.

Wannan karramawa da jama'ar Mandada suke yi masa yasa yake ganin yana da wata baiwa ce daga ubangijinsu, inda mutane daban-daban daga garuruwan Indiya suke zuwa wajensa domin samun waraka daga matsalolin dake damunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel