Tashin hankali: An kama wani saurayi da tsananin karfin sa yasa karuwa ta mutu a lokacin da yake saduwa da ita a otel

Tashin hankali: An kama wani saurayi da tsananin karfin sa yasa karuwa ta mutu a lokacin da yake saduwa da ita a otel

- Hukumar 'yan sanda ta kama wani saurayi da ake zargin ya kashe wata karuwa a lokacin da yake saduwa da ita a otel

- Wata ma'aikaciyar otel din ce ta gano gawar karuwar a lokacin da mutumin yake kokarin guduwa daga otel din

- Kwamishinan 'yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa suna bincike yanzu haka akan lamarin

Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta kama wani mutumi mai tsananin karfi wanda ya kashe wata karuwa a lokacin da yake saduwa da ita a otel a jihar ta Delta.

Mutumin da karuwar sun karbi hayar wani dakin otel a yankin Amukpe dake cikin karamar hukumar Sapele na jihar Delta. Wata mai aikin hotel din ce ta gano gawar karuwar jiya Alhamis 8 ga watan Agusta, bayan mutumin yayi kokarin fita daga otel din.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Adeyinka Adeleke ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa suna bincike yanzu akan lamarin da har yasa karuwar ta mutu.

KU KARANTA: Mariya Sunusi Dantata: Matar da ta zama baya goya marayu a kaf fadin Afirka wajen ciyar da mabukata

Wannan dai ba shine karo na farko da aka saba samun gawarwakin karuwai a dakunan otel ba, kwana uku da suka wuce mun kawo muku labarin yadda wani dan sanda yaso ya gudu ba tare da ya biya wata karuwa hakkinta ba bayan yayi amfani da ita.

Lamarin da ya jawo hankalin mutane masu dumbin yawa a yankin na jihar Legas, inda suka dinga yiwa dan sandan tofin Allah tsine, suka kuma kwace wasu daga cikin kayayyakinshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel