AMCON ta kara samun hurumi bayan rattaba hannun Shugaban kasa

AMCON ta kara samun hurumi bayan rattaba hannun Shugaban kasa

Shugaba Buhari ya karawa hukumar AMCON mai kula da kadarorin Najeriya karfi wajen karbo kudin bankuna da ke hannun wasu tsirarrun mutane wanda su ka karbi aro ba su maida ba.

Kamar yadda mu ka samu labari, shugaban kasar ya sanya hannu ne a kan wasu kudirori biyu da za su taimaka wajen karbo kudin bankuna da ke hannun masu cin bashin kudi su tsere a kasar.

Sanata Ita Enang wanda ke taimakawa shugaban kasa wajen harkokin majalisar dattawan Najeriya ya bayyana cewa an yi wa kudirin dokar da ta kafa AMCON garambawul a shekarar nan.

KU KARANTA: Fasa-kauri: Hameed Ali ya yi wani wawan kamu a Jihar Neja

Enang ya ce wannan sabuwar doka za ta taimaka wajen ganin an rika sa-wa wadanda a ke bi makudan bashi ido a banki. Hukumar AMCON za ta rika bibiyen duk asusun wannan mutane.

Haka zalika shugaban kasar ya rattaba hannu a kan kudirin nan na hukumar NBMA a Ranar Laraba, 7 ga Watan Agusta, 2019. Wannan doka zai dafawa hukumar AMCON wajen aikin ta.

Yanzu haka akwai wasu mutane da ba su wuce 20 ba da a ke bi bashin fiye da Naira tiriliyan 5 a Najeriya. Wannan doka da a ka kawo za ta sa hukumar AMCON ta rika bin kadinsu a bankuna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel