Tsaro: Manyan sojojin Amurka 13 na zagaye a Najeriya

Tsaro: Manyan sojojin Amurka 13 na zagaye a Najeriya

A yayin tumke damarar tabbatar da ingancin tsaro domin bunkasa harkokin yaki da ta'addanci a Najeriya, manyan dakarun sojojin 13 na kasar Amurka na ci gaba da zagaye da kuma gudanar da ziyarce-ziyarce a Najeriya.

Manyan jami'an gwamnati biyu na kasar Amurka na cikin tagawar dakarun sojin da ke ci gaba da gudanar da shawagi na tsawon makonni biyu a cikin Najeriya da kuma wasu kasashen duniya da suka hadar da Angola, Djibouti, Algeria da kuma Jamus.

Tagawar manyan gwamnatin kasar Amurka bisa jagorancin Janar John Paxton, Jr. mai ritayi, ta zaiyarci hedikwatar dakarun soji da ke garin Abuja a ranar Talata, 6 ga watan Agustan 2019, inda suka gana da manyan dakarun sojin kasar nan tare da mika godiyar wannan tarba da suka samu.

Cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka dake garin Abuja ya fitar a ranar Laraba, ya ce manufar wannan ziyara ba ta wuce tabbatar da hadin gwiwar tsaro ba a kasashen duniya. Ta kuma ce wani shiri da ya wajaba a tsarin gwamnatin kasar ya samo asali ne tun a shekarar 1986.

KARANTA KUMA: Tattalin arziki: Najeriya ba ta da wanda ya fi Buhari - Garba Shehu

A sanarwa da ofishin jakadancin ya fitar, "domin tabbatar da wannan manufa, gwamnatin kasar Amurka za ta ci gaba shimfida hannayenta na bayar da taimako ga gwamnatocin kasashen Afirka a suka hadar da Najeriya wajen kare kawunansu daga annobar ta'addanci."

Wannan tsari zai taimaka kwarai da aniya wajen inganta harkokin tsaro na cikin gida, bunkasa karfin ikon kasashe wajen kare kawunansu daga ta'addanci, magance aukuwar miyagun laifuka da ketare iyakokin kasa, fasakauri, fataucin miyagun kwayoyi da kuma cinikayyar dan Adam."

Kazalika wannan tsari da ya zamto al'ada zai ci gaba da bai wa gwamnatin kasar Amurka kyakkyawar fahimta a kan halin da kasashen da jami'anta suka ziyarta ke ciki.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel