Hotuna: Wasu tsofaffi sun bar tarihi yayin da suka shafe shekara 50 suna soyayya sannan suka angwance suna da shekaru sama da 90

Hotuna: Wasu tsofaffi sun bar tarihi yayin da suka shafe shekara 50 suna soyayya sannan suka angwance suna da shekaru sama da 90

- Wasu tsofaffin masoya 'yan kasar Ghana sun bar tarihi yayin da suka shafe shekara 50 suna soyayya babu aure sannan suka angwance a lokacin da suke da shekara 96 da kuma 93

- Masoyan sun samu 'ya'ya tara a lokacin da suke soyayyar, inda daga baya kuma suka yanke hukuncin suyi aure su karasa rayuwarsu a haka

- Faston da ya daura auren yayi bayanin cewa ya kamata tsofaffin su zama abin koyi domin kuwa babu yadda za ayi su kai wannan lokacin a tare ba tare da sun samu fuskantar juna ba

Wani mutumi dan kasar Ghana mai suna James K.Andorful, mai shekaru 96 da tsohuwar masoyiyarshi Margaret Manuel mai shekaru 93 sun angwance ranar Asabar dinnan da ta gabata 3 ga watan Agusta.

Mata da mijin sun sha soyayya sama da shekaru 50 da suka gabata, kuma wannan soyayya da suke sun haifi yara 9. Daga baya suka yanke hukuncin a daura musu aure, inda wani Fasto mai suna Rev. James Oko Barnor ya daura musu.

Hotuna: Wasu tsofaffi sun bar tarihi yayin da suka shafe shekara 50 suna soyayya sannan suka angwance suna da shekaru sama da 90
Lokacin daurin aure
Asali: Facebook

KU KARANTA: Tashin hankali: Saurayi da budurwa sun mutu bayan sun fado daga kan gada lokacin da suke rungume-rungume da sunbatar juna

Da yake wa'azi a wajen daurin auren, Rev Oko Barnor ya bayyana cewa mata da mijin sun kai wannan lokacin ne saboda sun samu fahimtar juna.

"Idan har masoya za su yi zama na shekara 50 a tare, hakan yana nufin sun fuskanci junansu sosai," in ji shi.

Hotuna: Wasu tsofaffi sun bar tarihi yayin da suka shafe shekara 50 suna soyayya sannan suka angwance suna da shekaru sama da 90
Bayan kammala daurin aure
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel