Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojan sama ta sayi kwararrun karnuka guda 21 (Hotuna)

Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojan sama ta sayi kwararrun karnuka guda 21 (Hotuna)

Rundunar Sojan saman Najeriya ta shigo da wasu kwararrun karnuka na musamman guda 21 daga kasar Afirka ta kudu wadanda suka samu horo a kan harkar binciko duk inda aka binne bamabamai, don habbaka yakin da take yi da yan ta’addan Boko Haram.

Haka zalika rundunar ta horas da wasu jami’anta guda 20, wadanda suka samu horo na tsawo makonni 13 a kan yadda zasu yi aiki tare da karnuna, wadanda ake kira ‘K-9’, su kuma Sojojin ake kiransu ‘K-9 handlers’.

KU KARANTA: Da na zauna da kishiya gara na kashe kaina – Inji wata Mata da mijinta zai kara aure

Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojan sama ta sayi kwararrun karnuka guda 21 (Hotuna)
Karnuka
Asali: Facebook

Legit.ng ta ruwaito karnukan sun shigo Najeriya ne a ranar Talata, 6 ga watan Agusta na shekarar 2019, daga cikin ayyukan da zasu yi akwai binciken inda aka binne ko boye bamabamai, binciken kwayoyi, gudun wuce sa’a don kama barawo, iyo a cikin ruwa da kuma aikin ceton rai.

A shekarar 2016 shugaban hafsan sojan sama, Sadique Abubakar ya kafa wannan sashi na karnukan K-9, kuma zuwa yanzu karnukan dake wannan sashi sun kai guda 60, wanda zuwa yanzu sun taimaka a bincike a tashoshin jiragen ruwan Najeriya, cibiyoyin sojan sama da yaki da ta’addanci.

Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojan sama ta sayi kwararrun karnuka guda 21 (Hotuna)
Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojan sama ta sayi kwararrun karnuka guda 21
Asali: Facebook

A wani labari kuma, rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas ta cika hannunta da fitaccen mawakin Najeriya, Augustine Kelechi wanda aka fi sani da Tekno saboda bayyana halin fitsara a bainar jama’a.

Yansanda sun kama mawakin ne a ranar Talata, 6 ga watan Agusta, inda ba tare da wata wata ba suka zarce dashi zuwa ofishin Yansanda masu gudanar da binciken manyan laifuka domin amsa tambayoyi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng