Dalibin jami'ar kimiya da fasaha ya kashe Almajiri a Kano

Dalibin jami'ar kimiya da fasaha ya kashe Almajiri a Kano

Wani dalibin jami'ar kimiya da fasaha KUST da ke jihar Kano, ya kashe wani dan Almajiri mai shekaru 18 a duniya, Adamu Ibrahim a kauyen Sabon Garin 'Yan Kwaya da ke karamar hukumar Wudil ta Kanon Dabo.

Jaridar Kano Today ta ruwaito cewa, dalibin mai sunan Lubsi ya kashe dan Almajiri Adamu yayin diban ruwa a wata rijiya daf da jami'ar da ke garin Wudil.

Wani mashaidin wannan mugun ji da mugun gani, Husaini Ibrahim, ya ce shi da marigayi Adamu sun kasance a bakin rijiyar yayin da cikin gadara Lubsi ya nemi su bashi wuri domin ya debi ruwa.

Rashin bin wannan umarnin ya sanya Lubsi ya yi amfani wani madoki na itace wajen sheme dan Almajiri Adamu.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, an garzaya da marigayi Adamu zuwa asibiti na kurkusa inda a nan ya ce ga garinku nan.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari.

DSP Haruna yace duk da wanda ake zargi ya yi aron kafar Kare, hukumar 'yan sandan za ta ci gaba da gudanar da bincike har sai ta tabbatar ya gurfana a gaban kuliya.

KARANTA KUMA: Cutar kanjamau ta kashe dan Najeriya Odemu Efe a kasar Habasha

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta kalato, babbar kotun jihar Kano ta yankewa wani matashi dan unguwar Tukuntawa, Umar Yakubu hukuncin kisa ta hanyar rataya a sanadiyar laifin kisan kai da ya aikata da almakashi.

Alkaliya wadda ta jagoranci zaman kotun a makon da ya gabata, Dije Abdu Aboki, ta zartar da wannan hukuncin kan Umar mai inkiyar Baban Mage biyo bayan laifin da ya aikata na kashe wani mutum, Ibrahim Adamu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel