EFCC ta kama Shugaban Manoma ya saci takin zamani da maganin feshin ƙwari a Garin Gunmi
A jiya ne EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa na reshen yankin Sokoto ta bayyana cewa ta kama shugaban kungiyar Manoman shinkafa na Garin Gumi a jihar Zamfara.
Hukumar EFCC ta cafke Rijia Ibrahim, da wasu mutane 2; Aminu Musa da Abdullahi Bashir ne bisa zargin karkatar da takin zamani da kuma maganin feshi na sama da miliyan N17, 100, 000.
EFCC ta ce Rijia Ibrahim ya hada kai ne da wani jami’in gwamnatin karamar hukuma mai suna Aminu Musa inda su ka saida kayan aikin noman jama’a ga wani ‘dan kasuwa, Aminu Musa.
Shugaban EFCC na shiyyar Sokoto da kewaye, Abdulahi Lawal, ya bayyanawa Manema labarai wannan inda ya ce sun gano cewa an karkatar da wannan kayan noma na Bayin Allah a Zamfara.
KU KARANTA: 'Yan Sanda sun damke tauraron Mawaki mai yawo da 'Yan mata tinbir
Lawal ya ce sun gano cewa wasu manyan motoci uku da ke dauke da takin zamani da kuma wata mota cike da maganin feshin ƙwari da ƙungiyar RIFAN su ka hada kudi su ka saya, sun yi dabo.
A cikin watan Maris ne wasu ‘yan kungiyar Manoman shinkafa na RIFAN da ke karamar hukumar Gumi su ka kai karar shugabansu Rijia Ibrahim da laifin saida kayan noman da su ka saya.
“Mun fara bincike tun wuri kuma mun gano cewa shugaban kungiyar Manoman shinkafan na Garin Gunmi, Rijia Ibrahim ya hada kai da wani ma’aikacin karamar hukuma wajen saida kayan.”
Hukumar ta EFCC ta yi wannan jawabi ne jiya Talata, 6 ga Watan Agusta, 2019. Bisa dukkan alamu dai za a maka wadannan mutane da a ke zargi ne da laifi a gaban kotu domin a hukuntasu.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng