Gwamna Abubakar ya shiga sahun musulmai masu gudanar da aikin Hajji a Saudiyya

Gwamna Abubakar ya shiga sahun musulmai masu gudanar da aikin Hajji a Saudiyya

Gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello ya wuce kasar Saudiyya a ranar Litinin, 5 ga watan Yuli domin gudanar da aikin Hajji ibadar Allah, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Gwamnan ya tafi ne a jirgin daya kwashe rukunin Alhazan jahar Neja na karshe zuwa kasar Saudi Arabia, inda yace ya yanke shawarar tafiya tare da Alhazan ne domin fahimtar matsalolin da suke fuskanta, da kuma hanyoyin magancesu.

KU KARANTA: Gwamnan jahar Borno ya kai ziyarar ba zata asibitoci da Asubah

Gwamna Abubakar ya shiga sawun musulmai masu gudanar da aikin Hajji a Saudiyya
Gwamna Abubakar
Asali: Facebook

“Tun da na zama gwamna a shekarar 2015, ban taba tafiya aikin Hajji tare da mahajjatanmu ba, don haka ina so na san yadda suke ji ne, da kuma yadda ake kulawa dasu, na samu rahotanni daga kwamitocin aikin Hajjin baya daban daban.

“Amma a yanzu nag a dacewar na tafi tare da alhazan, na gane ma idanuna da kaina don sanin idan akwai abin da za mu yi don inganta walwalar alhazanmu kafin tafiya na gaba.” Inji shi.

Gwamnan ya kara da cewa zasu gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya da cigaban arziki a jahar Neja dama Najeriya gaba daya, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Shima a nasa jawabin, Amirul Hajjin jahar Neja, Inuwa Musa Kuta ya bayyana cewa hukumar aikin Hajji ta jahar ta kara ma jami’an dake kulawa da walwalar alhazai alawus alawus dinsu domin su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Haka zalika ya yi kira ga jami’an da kuma alhazan dasu kasance jakadun jahar Neja nagari ta hanyar bin dokokin kasar Saudiyya sau da kafa, tare da mayar da hankulansu wajen gudanar da ibadojin dake tattare a cikin aikin Hajji.

Yayin da sakataren hukumar alhazan jahar Neja, Umar Makun Lapai ya kara da cewa jimillan alhazai 3,273 ne suka tafi aikin Hajji daga jahar Neja, daga ciki har da jami’an hukumar, daga karshe yace jahar za ta ciyar da alhazan abinci sau 3 a rana.

A wani labarin kuma, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a ranar Litinin, 5 ga watan Agusta, ya bar Abuja zuwa kasar Saudiyya domin shiga sahun miliyoyin Musulmai da za su yi aikin Hajji a fadin duniya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel