'Yan Indiya sun fara marhaban da zuwan El-Zakzaky

'Yan Indiya sun fara marhaban da zuwan El-Zakzaky

Rahotanni sun kawo cewa mutanen kasar Indiya sun fara murna da farinciki da batun zuwan Shugaban kungiyar yan Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, tun bayan da wata babbar kotun Kaduna ta bayar da belinsa domin ya je kasar don yin magani.

Tuni dai suka kirkiri wani maudu’i a shafin Twitter da alamar #IndiaWelcomesZakzaky wato dai Indiya na marhaban da zuwan Zakzaky.

A safiyar ranar Litinin, 5 ga watan Agusta ne dai kotun ta bai wa El-Zakzaki da uwargidarsa Zeenat damar zuwa kasar ta Indiya domin neman magani, kamar yadda lauyoyinsa suka bukata.

Damar da babbar kotun ta Kaduna ta bai wa Sheikh Ibrahim Zakzaky ta fita kasar waje tana tattare da wasu sharudda da kotun ta ce lallai sai an cika su.

Daya daga cikin sharuddan shi ne dole ne jami'an gwamnati su yi wa Zakzaky da matarsa rakiya zuwa Indiya.

Tun bayan kama shi a Disambar 2015, Indiyawa mabiya Shi'a sun bi sahun takwarorinsu na wasu kasashe musamman a yankin Gabas ta Tsakiya da Tekun Fasha, wurin nuna goyon baya a gare shi a shafukan saza zumunta.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya kashe abokinsa da ya fadi gasar karo-da-karo na rago bayan ya sa N500

Wannan ne ya sa wasu 'yan Indiya suke ta faman murna cewa mutumin da suka dade suna fafutukar neman a saki, yanzu zai je kasarsu domin neman magani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel