Tirkashi: Sabuwar rigima ta barke tsakanin Adam A Zango da wata matar aure da ta zagi amaryarsa

Tirkashi: Sabuwar rigima ta barke tsakanin Adam A Zango da wata matar aure da ta zagi amaryarsa

- Rigima ta barke tsakanin Adam A Zango da wata mata da ta nemi ta ci mutuncinsa dana matarsa a shafin Instagram

- Matar dai tayi wata magana ne a shafin na Instagram, bayan wani hoto da amaryar Adam Zangon ta wallafa inda tayi rubutun soyayya akan mijin nata

- Zango ya yiwa matar gargadi tare da neman mijinta ko 'yan uwanta su dauki mataki a kanta idan ba haka baa zai dauka da kanshi

A ranar Asabar ne 3 ga watan Agustan wannan shekarar, fitaccen jarumin Kannywood Adam A Zango, ya aikawa wata matar aure mai suna Misis Lawal Mahmud sakon gargadi, inda ya bukaci mijinta da 'yan uwanta akan su ja mata kunne akan yunkurin cin zarafinsa dana matarsa da ta yi, idan kuma ba haka ba shi zai dauki matakin da yaga ya dace.

Lamarin da ya jawo wannan gargadi da fitaccen jarumi yayi shine, amaryar jarumin mai suna Safiyya ta dora hoton mijinta tare da yin magana a kansa mai sanyaya zuciya a shafinta na Instagram, a wurin da ake bayyana ra'ayi kuwa sai kawai aka gano matar mai suna Misis Lawal ta yi rubutu a kasan wannan hoto da Amaryar Zango ta sanya, inda ta ce:

KU KARANTA: Tashin hankali: Ko kadan bana dana sanin kashe mahaifina dana yi, saboda shi ma da ya samu dama kashe ni zai yi - Aminu

"Baki da hankali ko kadan, indai Adam Zango ne gaki gashi nan har kike wani rawar jiki a kanshi, kwana kadan zaki zama bazawara."

Bayan wannan magana da ta wallafa, matar ta sake wallafa wata maganar cewa: "Yadda sauran matansa suka tafi kema haka lokacin ki zai yi ki tafi gidanku, amma ina yi miki addu'a Allah yasa ya daina domin ki samu ki cigaba da nuna mishi soyayya."

Alamu sun nuna cewa wannan rubutu da matar ta yi bai yiwa jarumin dadi ba ko kadan, domin kuwa a take ya dauki hotunan rubutun da matar tayi sannan ya nemo hotunanta ya wallafa a shafinsa, sannan a kasa yayi rubutu ya ce:

"Zaku iya zagina yadda kuka ga dama, amma kada ku saka matata a cikin wannan tsanar da kuke nuna mini, ita ba 'yar fim bace, bani da alaka da ita haka kuma matata ba ta da alaka da ita, kuma matar aure ce, suna nan da yawa da suke son ganin na rabu da matata don su cigaba da zagina, saboda haka ina so mijinta ko 'yan uwanta su ja mata kunne ko kuma ni na dauki matakin da ya dace."

A karshe jarumin ya ce matarsa ba 'yar fim ba ce tana da damar da zata bayyanawa duniya irin soyayyar da take yiwa mijinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel