Bashin Tiriliyan 1.25 ya hau kan wuyan Jihohi masu arzikin man fetur
Rahotan da jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna cewa wasu daga cikin manyan jihohin da ke samun kaso mafi tsoka daga asusun gwamnatin Najeriya su na dauke da tarin bashin kudi a halin yanzu.
Binciken da a ka yi ya nuna cewa a farkon 2019, a na bin jihohi masu arzikin man fetur bashin Naira tiriliyan 1.25. Jihohin sun karbi wannan bashi ne duk da kasonsu ya fi na kowa yawa a kasar.
Ma’aikatar kudin Najeriya ta ce daga shekarar tsakiyar 1999 zuwa karshen 2018, wadannan tsirarun jihohi sun karbi Naira tiriliyan 44.68 daga asusun tarayya a matsayin kason man fetur.
Wannan kudi bai kunshi ainhin abin da a ke rabawa kowace jiha a duk wata ba. Misali a 2018, jihohin Neja-Delta sun samu Biliyan 100 zuwa 200 daga hannun asusun gwamnatin tarayya.
KU KARANTA: Kotu ta karbe kadarori da akawun din wani kamfani saboda tarin bashi
A na warewa jihar da ke da arzikin man fetur karin 13% daga cikin abin da a ka samu duk wata. Sai dai kuma wannan bai hana su cin makudan bashi daga bankunan gida da kasashen waje ba.
Jihohin da ke da man fetur a Najeriya su ne; Akwa Ibom, Ribas, Bayelsa, Kuros Ruba, Delta da kuma Edo. Sauran jihohin sun hada Imo, Abia da kuma Ondo. Su ne a ke bi wannan tarin bashi.
Alkaluman da ofishin da ke kula da bashin Najeriya, DMO ya fitar ya nuna hakan. Wadannan jihohi sun fi kowane bashi a wuyayansu duk da cewa su ne su ka fi samun kudi a fadin kasar nan.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng