Bayan watanni biyar da haduwa a Twitter, saurayi da budurwa sun gama shiri tsaf domin angwancewa

Bayan watanni biyar da haduwa a Twitter, saurayi da budurwa sun gama shiri tsaf domin angwancewa

- Saurayi da budurwa da suka hadu a shafin sada zumunta na Twitter sun gama shiri tsaf domin auren junansu

- Haduwar ta su wacce duka-duka ba ta fi watanni biyar tayi karfi bayan budurwar ta tura mishi sakon lambarta

- Saurayin yace bai fi watanni biyar da haduwarsu ba ya nuna yana son aurenta kuma ta amince

Wasu saurayi da budurwa da suka hadu a shafin sada zumunta na Twitter watanni biyar da suka gabata sun gama shiri tsaf domin angwancewa.

Wani mutumi mai suna @mudeekings ya bayyana wannan lamari a shafinsa na Twitter, inda ya sanya hoton budurwar ta sa wacce ya nemi aurenta bayan watanni biyar da haduwarsu a shafin Twitter.

"Na yi mata magana bayan watanni biyar da haduwar mu, kuma ta bada goyon baya."

KU KARANTA: Tirkashi: Shehu Sani ya yi maganna akan gawarwakin sojoji 1,000 da aka binne a boye

Ga sakon da ya aika mata farkon haduwarsu:

"Ina fatan kina lafiy? Babban dalilin rubuto miki wannan sako shine na sanar dake ina matukar son nayi miki magana ta waya, ban san ko zaki bani lambarki ba."

Da aika mata wannan sako bata yi kasa a guiwa ba sai ta aiko masa da lambarta, daga nan ne soyayyar tayi nisa har ta kawo su wannan matakin na aure.

Kwanakin baya ma dai an samu wasu saurayi da budurwa daga Kano da aka daura musu aure a shafin Facebook, lamarin da ya kawo kace-nace a shafukan sada zumunta da kuma kasar Hausa baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel