Rayuwa mai albarka: Dattijon da ya rubuta Al-Qur'ani sau 70 da hannayensa

Rayuwa mai albarka: Dattijon da ya rubuta Al-Qur'ani sau 70 da hannayensa

- Wannan Dattijo da kuke gani yana zaune da iyalinshi ne a cikin talaucin rayuwa, amma kuma talaucin bai hana shi bautawa ubangijinsa ba

- Rahotanni sun nuna cewa Dattijon ya rubuta Al-Qur'ani sau Saba'in da hannayensa masu albarka

- Akwai kuma lokacin da aka tabbatar da cewa ya rubuce Al-Qur'anin daga Baqara zuwa Nasi a cikin kwana Sittin

Alhaji Shu'aibu Sa'eed Usman mutumin arewacin Najeriya ne, wanda yake da kimanin shekaru 80 a duniya. An tabbatar da cewa ya rubuta Al-Qur'ani daga Bakara zuwa Nasi sau 70 a rayuwarsa.

An ruwaito cewa akwai lokacin da ya taba rubuta AL-Qur'ani izu sittin a cikin kwana 60 kacal. Wannan shine mafi karancin lokacin da ya taba dauka yana rubutun Al-Qur'ani mai girma.

Alhaji Shu'aibu da iyalinsa suna zaune a wani karamin dakin soro. Kullum wuni yake yi cikin tilawa da rubuta Al-Qur'ani a daki daya, sannan da dare sai ya kwana a daya dakin.

KU KARANTA: Ba sani ba sabo: An dakatar da shugaban karamar hukuma da Hakimi a jihar Zamfara

Labarin wannan bawan Allah ya yadu a kasashen Larabawa shafukan sada zumunta da kuma dandalin ajiye bidiyo na Youtube. Sannan akwai lokacin da wani Balarabe ya ziyarce shi har gidansa yayi hira dashi.

Larabawa sun yi mamakin samun irin wannan mutumi mai baiwa haka duk kuwa da kasancewarsa a cikin talauci.

Alhaji Shu'aibu kwararrene a fannin Al-Qur'ani ya san adadin kowacce kalma da kuma wuraren da suke a cikin Al-Qur'ani, sannan kuma nan take idan ka tambayeshi zai fada maka sannan yayi bayani daga inda kalmar ta fara zuwa inda ta tsaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel