Babbar magana: Wata mata ta auri dan cikinta, saboda ta kashe mishi makudan kudade lokacin karatunshi

Babbar magana: Wata mata ta auri dan cikinta, saboda ta kashe mishi makudan kudade lokacin karatunshi

- Wata mata 'yar kasar Malawi ta fito da wani sabon salon lamari, inda ta auri dan da ta haifa na cikinta

- Matar ta ce ta yi hakan ne domin ta kashe masa makudan kudade a lokacin da yake karatunshi, saboda haka ba za ta bari wata ta raba ta dashi ba

- A yanzu haka dai komai ya kankama tsakanin uwa da dan, yayin da suke zaune gida daya a matsayin mata da miji

Wata mata 'yar asalin kasar Malawi da aka bayyana sunanta da Memory Njemani wadda ke da shekaru 47 da haihuwa ta auri danta na cikinta.

Jaridar Nyasa Times ce ta ruwaito wannan laari inda take cewa Njemani ta bayyana cewa ta kashewa dan nata mai shekaru 30 a duniya kudi masu yawan gaske a harkokin karatunsa, hakan ne yasa ta yanke shawarar aurensa domin kada wata mata ta aure shi ta raba ta dashi, bayan kuma ita ce ta san wahalar shi, dan haka ita ce za ta san dadinshi.

KU KARANTA: Ba sani ba sabo: An dakatar da shugaban karamar hukuma da Hakimi a jihar Zamfara

Bugu da kari ta bayyana cewa wannan shi ne lokacin da za ta huta ma rayuwarta tare da danta saboda sun yi aiki tukuru don ganin sun kai ga cimma muradunsu na rayuwa.

A halin yanzu dai zamantakewar uwar da danta a matsayin mata da miji ta yi nisa domin kuwa suna zaune ne a gida daya suna more rayuwarsu kamar dai yadda sauran ma'aurata ke rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel