Jam’iyyar APC na fuskantar barazanar sauyin sheka da yawa a wata jihar arewa kan nade-naden mukamai

Jam’iyyar APC na fuskantar barazanar sauyin sheka da yawa a wata jihar arewa kan nade-naden mukamai

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Niger na barazanar kaurace ma jam’iyyar akan abunda ta bayyana a matsayin rashin sakawa masu yiwa jam’iyyar biyayya ta hanyar basu mukamai.

Hakan na kunshe ne a cikin hukuncin da aka yanke a taron kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wanda ya kudana a sakateriya jam’iyyar, inda aka gabatar da kwafin takardar ha manema labarai a ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta.

A hukuncinsu dauke da sa hannun sakataren labaranta, jam’iyyar reshen jihar ta nuna rashin jin dadita akan matakin gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, wanda bai tuntubi jam’iyyar ba maimakon haka sai yayi yadda yake so shi kadai ba tare da amincewwar jam’iyyar ba domin yiwa wanda ba dan jam’iyya bane, wato Amb. Zubairu Dad, wanda ya kasance dan PDP da yayi adawa day an takarar APC a zaben da ya gabata alfarmar samun mukamin minista.

Ta kuma lura cewa zababben ministan da Sanata mai wakiltan Niger ta gabas, Sanata Mohammed Sani Musa sun fito ne daga karamar hukuma guda ta Paikoro, sannan mazzabarsu da yankinsu guda wanda hakan ya saba ma kundin tsarin jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: An ga jaririn watan Dhu'l-Hijjah a kasar Saudiyya

Don haka, a hukuncin da suka yanke a taron wanda ya samu halartan dukkani shugabanni kananan hukumomi da sakatarori 25, jam’iyyar APC na jihar tayi kira ga janye mukamin zababben ministan sannan a maye gurbinsa da mamban jam’iyyar wanda yayi aiki domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a lokacin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel