Manyan dalilai 5 dake sa mata cin amanar mazajensu na aure

Manyan dalilai 5 dake sa mata cin amanar mazajensu na aure

Duk da ba kasafai mata ke cin amanar aure ba idan aka kwatanta da maza, kuma ba kasafai ake kama su ba idan har ba cigaba suka yi da aikata hakan ba, akwai wasu dalilai dake saka mata cin amanar mazajensu. Manya daga cikin dalilan su ne;

1. Burus da al'amuran matar ka: Masana halayyar dan adam sun gano cewa mata sun fi maza bukatar soyayya da kauna da son a kula su. Mata kan shiga damuwa duk lokacin da mijinsu ko masoyi ya yi burus da al'amuransu. Yin burus da al'amuran mace kan sa ta saki jiki da wani namijin da ya nuna damuwa da al'amuranta, wanda hakan kan iya jawo wa ta ci amanar masoyinta ko mijinta.

2. Tsohuwar soyayya: Wasu lokuta haduwa da tsohon masoyi kan yi tasiri a kan mace, musamman idan ya kasance tsohon masoyin ya yi tasiri a rayuwar ta. Yana da kyau miji ya tsare matarsa haduwa da tsohon masoyinta.

3. Daukan fansar cin amana: Wasu matan aure na cin amanar mazansu ne domin daukan fansar cin amanarsu da maza ke yi.

Wani bincike na masana ya nuna cewa da yawan mata na sakin jiki da wasu mazan a dandalin sada zumunta ko wuraren aiki domin su dauki fansar cin amanarsu da maza ke yi.

4. Neman gamsuwar jima'i: Wanna kusan shine babban dalilin da ke saka mata da yawa cin amanar mazajensu.

Masana mu'amar aure sun shawarci ma'aurata suke tattauna al'amuran da suka shafi kwanciya domin sanin hanyoyin da zasu gamsar da junansu domin guje wa cin amanar juna a cikin zamansu.

5. Kudi: Wasu kuma matan na cin amanar mazajensu ne domin son kudi. Ba kasafai ake yi wa mace uzuri ba idan ta ci amanar aure saboda kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel