Ganduje da Abba Gida-Gida: Shugaban PDP bai samu ikon bayar da shaida a kotu ba

Ganduje da Abba Gida-Gida: Shugaban PDP bai samu ikon bayar da shaida a kotu ba

Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party na jihar Kano, Rabiu Suleiman Bichi ya gurfanar gaban kotun sauraron karar zaben gwamna a jihar a ranar Alhamis domin bayar da shaida kan kallubalantar nasarar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar.

Sai dai shugaban na PDP bai samu ikon bayar da shaidan ba a gaban kotun saboda korafi da lauyan da ke wakiltan Gwamna Ganduje da jam'iyyarsa ta APC, Aliyu Umar (SAN) ya yi.

Barrister Aliyu Umar (SAN) ya shaidawa kotu a ranar Alhamis cewa kafin ranar Alhamis bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar cewar ba za su gabatar da shaidu ba har sa an gyara wasu kura-kuren rubutu da kotun daukaka kara ta Kaduna ta yi magana a kai.

DUBA WANNAN: Zaben Kano: Kotu ta aike wa INEC da Kwamishinan 'Yan sanda sammaci

Ya ce bangarorin biyu sun amince da cewa shugaban na PDP da wasu mutane bakwai za su bayar da shaidansu ne a ranar 5 ga watan Augusta amma ya yi mamakin ganin sun gabatar da shugaban na PDP a kotu a ranar 1 ga watan Augusta domin bayar da shaida.

Jagoran lauyoyin PDP, Awomolo (SAN) ya shaidawa kotu cewa iya sanin sa babu wara dokar kotu da ta haramtawa shugaban na PDP bayar da shaida kuma ya roki kotu tayi watsi da bukatar wadanda akayi karar.

Alkaliyar kotun, Justice Halima Shamaki ta ce bayyanan da aka gabatarwa kotun a fili su ke na cewa kotun ta bayar da umurnin a gabatar da takardun da kotun kolin na Kaduna ta ce a gyara kafin ranar 3 ga watan Augusta.

Ta kuma daga cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Augusta domin a gabatar da dukkan shaidu 8 a gaban kotun saboda adalci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel