Gwamnatin tarayya ta jinjina wa wasu jihohin Najeriya biyu, ta fadi dalili

Gwamnatin tarayya ta jinjina wa wasu jihohin Najeriya biyu, ta fadi dalili

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Obasanjo, ya ware jihar Kano da Legas daga cikin sauran jihohin Najeriya tare da yi musu jinjina.

Da ya ke gabatar da jawabi a wurin wani taro a Legas ranar Laraba, Osinbajo ya ce jihohin biyu sun zama abin koyi wajen rungumar dukkan 'yan Najeriya a biranensu, lamarin da ya ce ya na kara kawo musu cigaba da kara inganta zaman lafiya a cikin kasa.

A cewarsa, "tabbas zaman hadakar kabilu daban-daban kan iya haifar da zaman lafiya da kulluwar zumunci ko kuma haddasa rikici, kamar yadda ta sha faruwa a wurare daban-daban a fadin duniya.

"Yawan kabilu daban-daban a cikin kasa daya ba matsala ba ne, ana samun matsala ne ta yadda kabilun suka mu'amalanci junansu. Nasarar mu a matsayin kasa guda mai kabilu da yawa ta dogara a kan yadda muka jibanci lamuran junan mu."

Da ya ke bayar da misalin jihohin Najeriya da suka yi amfani da banbacin kabila wajen samar wa kansu cigaba, Osinbajo ya ce, "cigaba da habakar tattalin arzikin jihohin Kano da Legas ya na da alaka da rungumar kabilu daban-daban da suka yi a biranensu.

DUBA WANNAN: Gwamnatin kasar Kenya ta kori Yesu, ta kama faston da ya gayyato shi

"Kasancewar Legas a matsayin daya daga cikin jihohin Najeriya da ke da iyaka da kasashen ketare ta hanyar ruwa, ya bata dama wajen zama cibiyar kasuwanci ta kasashen nahiyar Afrika, amma babban sirrin cigaban jihar shine ta yadda kowa nata ne matukar zai yi harkokinsa bisa biyayyar ga doka da tsarin kasa.

"Kano cibiya ce ta kasuwanci da 'yan kasuwa ke zuwa tun daga gabas ta tsakiya da kasashen yammacin Afrika, amma sirrin nasarar kasuwancin jihar shine bawa bakin kabilu dama su yi kasuwancinsu da bai saba da dokokin kasa ba."

Kazalika, ya sake yaba wa jihohin bisa kokarinsa wajen bayar da mukaman siyasa ga 'yan kabilun da ba 'yan asalin jiharsu ba, tare da bayyana cewa hakan ya haifar da zama lafiya da kaunar juna a tsakanin asalin mutanen jihohin da bakin da suke zaune a biranen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel