Dangote ya rabawa ‘Yan wasan Najeriya kyautar $50, 000 bayan Gasar AFCON

Dangote ya rabawa ‘Yan wasan Najeriya kyautar $50, 000 bayan Gasar AFCON

Kamar yadda labari ya zo mana, shugaban kamfanin nan na Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya cika alkawarin da ya yi wa ‘yan wasan Najeriya na cewa zai ba su kyautar makudan kudi.

Kwanan nan ne a ka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afrika inda Super Eagles na Najeriya ta zo na uku. A lokacin da a ke gasar Dangote ya yi alkawarin ba ‘yan kwallon Najeriya gudumuwa.

Yanzu babban mai kudin na Nahiyar Afrika ya bada wadannan kudi kamar yadda ya yi alkawari. Babban jami’in kamfanin Dangote, Olakunle Alake, shi ne ya wakilci Hamshakin Attajirin.

Olakunle Alake ya bada takardar karbar kudi a banki ne ga wasu daga cikin manyan masu horas da ‘yan wasan Super Eagles wadanda su ka hada da Chidi Ngoka da kuma Dayo Achor Enebi.

KU KARANTA: Mohamed Salah da Sadio Mane sun shiga sahun manyan 'Yan kwallon Duniya

‘Dan kwallon Najeriya, John Ogu ya na nan a lokacin da a ka bada wannan kyauta kamar yadda rahotanni su ka zo mana daga jaridar Vanguard a Ranar Laraba watau 31 ga Watan Yuli, 2019.

Aliko Dangote ya yi alkawarin cewa zai ba ‘yan kwallon Super Eagles kyautar Dala 50, 000 a kan duk kwallon da su ka zura a wasa na daf da karshe. Aljeriya ta doke Najeriya ne da ci 2-1 a wasan.

Haka zalika wani babban Attajirin kuma Aminin Dangote, Femi Otedola, ya yi wa Super Eagles alkawarin Dala $25, 000 a wannan wasa. A karshe dai Riyadh Mahrez ya yi waje da Najeriya.

A kudin Najeriya, abin da kungiyar Super Eagles din za ta samu ya kai kusan Naira miliyan 18 a hannun Alhaji Aliko Dangote. Shi ma Femi Otedola ya bada abin da ya kusa kai Naira miliyan 10.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng