'Yan Afrika birai ne - Tsohon shugaban kasar Amurka

'Yan Afrika birai ne - Tsohon shugaban kasar Amurka

A cikin wani faifan nadar sautin murya da jaridar The Atlantic ta wallafa a shekarar 1971, an ji tsohon gwamnan jihar California kuma tsohon shugaban kasar Amurka ya kira 'yan Afrika birai bayan wakilan kasashen Afrika a majalisar dinkin duniya sun fusata shi.

Tsohon shugaban kasar, Ronald Reagan, ya bayyana hakan ne yayin wata hirarsa ta wayar tarho da tsohon shugaban kasar Amurka, Ricahrd Nixon.

Reagan ya furta wadannan kalaman batanci ne ba tare da sanin cewa Nixon na nadar dukkan hirar da suke yi ba.

Tsohon gwamnan ya harzuka ne bayan wakilan kasashen Afrika a majalisar dinkin duniya sun ki goyon bayan hadakar yin aiki tare tsakanin kasashen Amurka da China.

Bayan an sanar da sakamakon kuri'un da wakilan kasashen majalisar dinkin duniya suka kada ne, sai mambobin masu wakiltar kasar Tanzania suka fara tikar rawa a zauren majalisar dinkin duniyar.

DUBA WANNAN: Gwamnatin kasar Kenya ta kori Yesu Almasihu, ta kama faston da ya gayyato shi

Kwana daya da faruwar hakan ne sai Reagan ya kira shugaba Nixon domin ya tambaye shi ko ya kalli yadda kada kuri'ar ya gudana a zauren majalisar dinkin duniya.

"Ka kalli yadda biran nan na kasashen Afrika, da har yanzu ko takalmi ba su iya saka wa ba, ke zaune cikin annashuwa," a kalaman

An ji shugaba Nixon ya fashe da dariya bayan Reagan ya furta wadannan kalamai.

Wani farfesan tarihi a jami'ar birnin New York, Mista Tim Naftali, ne ya wallafa faifan sautin muryar bayan mutuwar Reagan a shekarar 2004.

Farfesa Naftali ya kasance mai kula da dukkan sautikan tsohon shugaba Nixon daga 2007 zuwa 2011.

Sai dai, an boye faifan kalaman batancin Reagan saboda dalilan tsaro a lokacin da ya ke raye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel