An kama wani barawo da ya shiga cikin silin din banki a Kebbi

An kama wani barawo da ya shiga cikin silin din banki a Kebbi

Dubun wani mutum da ya shiga cikin silin din bankin 'Guaranty Trus Bank (GTB)' a Birnin Kebbi da niyyar labe wa domin yin sata bayan an rufe bankin.

Mutumin da aka bayyana sunansa da Idam Jeremiah ya samu damar shiga cikin silin din ne bayan ya shiga bankin kamar yadda kowa ke shiga domin gudanar da hada-hadar kudi.

Wani shaidar gani da ido da ya nemi a boye sunansa, ya ce, "mutumin ya fake da shiga bandaki ne, ta inda ya samu ya tsallaka zuwa cikin silin din."

Majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewa wata mai shara ce a bankin ta fara jan hankalin shugabanninta, bayan ta ga takalma a bandakin da kuma sahun kafafu a jikin bango.

DUBA WANNAN: Ango ya saki amaryarsa a wurin walimar daurin aurensu

"Ita ce ta kira hankalin jami'an tsaron da ke aiki a bankin, kuma da daya daga cikinsu ya leka sai ya ga akwai mutum a labe a cikin silin." a cewar majiyar.

Majiyar ta bayyana cewa bayan an gano mutumin ne sai manajan bankin ya kira 'yan sanda, amma duk da haka mutumin ya ki yarda ya fito, sai da suka yi barazanar harbinsa idan bai fito ba.

Kakakin rundunar 'yan sandar jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin ga majiyar mu.

"Har yanzu sashen binciken manyan laifuka (CID) na gudanar da bincike a kan maganar," a cewar DSP Abubakar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng