Ci gaba: Yan N-Power 500 sun ajiye aiki a jihar Zamfara

Ci gaba: Yan N-Power 500 sun ajiye aiki a jihar Zamfara

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane 500 da suka amfana da shirin N-Power ne ajiye aikin a Jihar Zamfara bayan sun samu aikin yi na dindindin.

Shugaban Hukumar SIP na Jihar Zamfara Kabiru Umar ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Gusau, babban birnin Jihar a ranar Talata, 30 ga watan Yuli.

Ya bayyana cewa wadanda suka ajiye ayyukan na su sun samu aiki ne a karkashin gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jiha da wasu hukumomi daban-daban.

Umar ya kara da cewa dauki yan N-Power har 11,122 tsakanin 2016 zuwa 2017 a jihar Zamfara. An dauke su ne a bangarorin ayyuakan lafiya da noma.

Shugaban na SIP ya kara da bayyana cewa wasu ma’aikatan sa-kai su 321 ma an dauke su a karkashin N-Power, inda suka yi ayyukan na’urorin kwamfuta da sauran fasahohin da suka danganci zamani.

Sai dai kuma ya yi tsokacin cewa saboda rashin wadatattun motoci, akwai matsala sosai wajen yadda za a iya bi gari-gari ana yin duba-garin ayyukan wadannan masu ayyukan sa-kai a karkashin N-Power din.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ahmad Lawan ya bayyana sunayen shugabannin kwamitocin majalisar dattawa da mataimakansu

“Mu na ci gaba da samun korafe-korafe daga wasu shugabannin makarantun firamare da na sakandare cewa wasu ma’aikatan na N-Power su na fashin zuwa makarantu koyarwa. To amma babu yadda za mu yi, saboda mu na fama da karancin motocin zirga-zirgar da za mu iya zuwa duba-gari.”

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara ta taimaka musu da motocin zirga-zirgar gudanar da ayyukan su, ciki har da zagayen duba-garin ma’aikatan su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel