Kannywood: Abubuwa da ba ku sani ba kan tsohuwar jaruma Safiya Musa

Kannywood: Abubuwa da ba ku sani ba kan tsohuwar jaruma Safiya Musa

Safiya Musa, ta kasance fittaciyyar tsohuwar jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood. Kamar dai yadda labari ya nuna tun farko dai jarumar ta shiga harkar fim ne ba wai don neman kudi ba, sai dai domin rama wulakancin da take zargin wata yar fim tayi mata a Kaduna.

Sai ta sha alwashin ramawa ta hanyar shiga masana’antar a matsayin jaruma, kuma Allah da ikonsa sai Safiya ta shiga da kafar dama domin sai da ta dusashe tauraruwar waccar jarumar da ta shiga harkar domin ita.

Amma kuma jarumar na tsaka da haskawa a dandalin sai kawai aka fatattakesu wajen su goma ciki harda Kubra Dakko da Maryam Hiyana sakamakon wani lamari da ya taso, kamar yadda majiyarmu ta al’ummata ta bayyana.

Bayan barinta masana’antar sai ta sami miji tayi aure. wanda har yanzu tana gidan mijinta tare da kyawawan ‘yayansu.

KU KARANTA KUMA: Kamar koda yaushe: Gwamnan Borno ya kai ziyarar bazata manyan asibitocin jihar a cikin dare

Ganin yanda rayuwa ta canja mata ne yasa tace: “duk jarumar da ta sami miji tayi aure, idan ba haka ba akwai lokacin da zai zo ba fim din ba auren.

“Tabbas, aure lokaci amma lokacin tare suke tafiya da niya. akwai mata na kannywood wanda basu da niyar aure, amma sai suce lokacine baiyi ba,” inji Safiya Musa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel