Boko Haram: Mutane fiye da 60 sun mutu, 11 na asibiti bayan hari
Mun samu labari cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun yi sanadiyyar da Mutum fiye da 65 su ka bakunci barazahu a sabon harin da ‘yan ta’addan su ka kai a jihar Borno a karshen makon nan.
Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Trust, ‘yan ta’addan sun kai wannan hari ne bayan kashe masu mutane 11 tare da karbe makaman su da Sojoji su ka yi a makon da ya wuce.
Shugaban karamar hukumar Nganzai, Mohammed Bulama, shi ne ya bayyana cewa sun rasa mutane akalla 65. Shugaban karamar hukumar ya bayyanawa gwammnan jihar wannan ne a jiya.
A Ranar 29 ga Watan Yuli, 2019, shugaban wannan karamar hukumar ta Nganzai ya hadu da Mai girma gwamna Babagana Zulum wanda ya je ta’aziyya Garin Gajiram inda a ka yi wannan barna.
Har yanzu an nemi wasu an rasa bayan harin da ‘yan ta’addan su kai wannan Gari kwanaki. Mutane da-dama kuma yanzu su na faman jinya dauke da munanan raunuka daga harin.
KU KARANTA: Wasu 'Yan bindiga sun yi mummunan ta'adi a Jihar Kebbi
Gwamna Zulum ya yi Allah-wadai da harin, inda ya sake shan alwashin kare mutanen jihar daga Boko Haram, tare da yi wa wadanda a ka rasa addu’a da kai wa marasa masu jinya ziyara.
Mutane fiye da 10 ne su ke jinya a babban asibitin kwararru da ke Garin Maiduguri bayan wannan hari na ‘yan ta’adda. Akwai mutane kusan 60 da a ka kashe nan-take bayan harin na Boko Haram.
Rahotanni sun nuna cewa Boko Haram ne su ka kai wannan hari domin rama abin da ‘yan kato-da-gora su ka yi masu na kashe Mayakansu 11 kwanaki har ta kai wasunsu su ka ci kafar kare.
Mafi yawan wadanda a ka kashe din sun dawo ne daga jana'izar wasu Mamatan a Garin Nganzai da ke cikin Arewacin jihar Borno kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto a yau 29 ga Watan Yuli.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng