Likitoci sun ciro sarka 69, dan kunne 80 da kwabbai 46 a cikin wata mata
- Likitoci a kasar India sun yi matukar girgiza bayan sun gano wasu sarkoki da dan kunne da wasu tarkace masu yawa a cikin wata mata
- Matar, Runi Khatun, mai shekaru 26 ta gaza cin abinci kafin daga bisani ta fadi a sume bayan ta hadiye tarkacen a cikin ta
- Daga cikin abubuwan da likitoci suka gano a cikin ta akwai sarka guda 69, dan kunne 80, barimar hanci guda 11 da kwabbai 46 da wasu ragowar tarkace
Wata mata da aka garzaya da ita asibiti a kasar Indiya bayan jikinta ya yi laushi tare da kanjame wa ta girgiza likitoci yayin da suka gano sarkoki da tsabar kudi (kwabbai) da ta hadiye a cikinta bayan sun yi mata tiyata.
Matar, Runi Khatun, mai shekaru 26, wacce aka yi wa tiyata a asibitin gwamnati da ke kasar India, an ciro sarkoki 69, dan kunne 80, barimar hanci 11, agogo guda daya, kwabbai 46 da sauran wasu tarkace da ta hadiya a cikin ta.
A cewar jaridar kasar Ingila (Daily Mail UK), matar ta sanar da mahaifyarta cewa ta na jin kasala kuma ga shi ba ta iya cin abinci kafin daga bisani ta fadi a sume, lamarin da yasa aka garzaya da ita zuwa asibiti.
A cikin dakin aka yi mata tiyata ne likitoci suka fara fito da sarkoki da kwabban da matar ta hadiya, lamarin da su kan su likitocin ya girgiza su.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng