To fah: Babban burina a rayuwa shine na ganni a dakin mijina - Jaruma Teema Yola
A wata hira da jaridar Aminiya ta yi da fitacciyar jarumar wasan Hausa ta Kannywood, Fatima Isah Muhammad wacce aka fi sani da Teema Yola. Ta bayyana yadda ta yi suna a duniyar fim
Jarumar wacce ta fito da sunan Hajiya Laure a cikin fitaccen fim dinnan na Mansoor, wanda ya zama daya daga cikin manyan fina-finai da aka taba yi a masana'antar Kannywood. Yanzu haka dai tauraruwar jarumar na kara haskawa a duniyar fim.
Ga yadda hirar ta su ta kasance da jaridar Aminiya:
Aminiya: Ya aka yi kika fara wannan sana'a?
Teema: Na shiga harkar fim ne saboda ina sha'awar sana'ar sosai. Ban taba boye soyayyar da nake yiwa kaina na ganin na zama jaruma ba, kuma sai nayi sa'a daya daga cikin manyan marubutan masana'antar, Abdulkarim Papalaje sai ya hada ni da wasu masu shirya fina-finai na masana'antar. Suka gwada ni, da yake abu ne da nake so sosai sai gashi na basu mamaki sosai.
Yanzu maganar nan da nake daku ban san iya fina-finai nawa na fito a cikinsu ba. Na san shaharar da nayi a masana'antar ba yin kai na bane, yin Allah ne, kuma ko da yaushe ina yi masa godiya da wannan ni'ima da yayi mini; wannan ita ce shekarata ta bakwai a wannan masana'anta.
Aminiya: Gaya mana irin fadi tashin da kika sha a wannan masana'anta?
Teema: Na sha fama sosai kafin na samu damar shigowa wannan masana'anta. Akwai lokuta da dama da za a sanya ni a fim, bayan anyi an gama komai, a karshe sai a hanani kudina. Zan iya yina akan a biya ni, amma wallahi baza su biya ni ba.
A lokuta da dama, mutane sukan bani shawarar na shigar da kara, amma kawai sai nayi dariya na manta da zancen. Daga baya sai na zo na gane cewa ana yi mini haka ne saboda ni sabuwar 'yar wasa ce, amma yanzu mutanen da suke hanani kudin nawa a da sune suke fara biyana tun kafin ma a fara shirin fim din.
KU KARANTA: Tashin hankali: Dan wasan Arsenal, Mesut Ozil ya sha da kyar, bayan wani hari da 'yan fashi suka kai masa zasu kashe shi
Aminiya: Wasu na cewa ana biyan ki da tsada kafin ki yadda ki fito a fim, shin gaskiya ne?
Teema: Dan kana tuka mota mai tsada, ko kana siyan abubuwa masu tsada ba hakan ne yake nuna cewa kai kai mai tsada bane a wajen aikin ka. Ni jaruma ce da nake kokarin ganin na kare mutuncina a koda yaushe, ina jin hakan ne yasa mutane suke mun wani kallo na daban.
Aminiya: Me zaki ce game da cigaban da kika samu a matsayinki na jaruma?
Teema: Cigaban dana samu a masana'antar Kannywood suna da yawa, amma zan iya cewa na je wurare masu yawan gaske, wadanda inda ace ban shiga harkar fim ba babu yadda za ayi naje wadannan wurare. Na hadu da manyan mutane da kuma masoya wadanda suke son ganin sun yi mini duk abinda nace ina so.
Aminiya: Hakan na nufin kin gama cimma burinki na rayuwa kenan?
Teema: Eh kusan haka, amma babban burina shine naga nayi aure na zauna a gidan mijina. Amma kuma ba zan daina harkar fim ba koda nayi aure. Zan cigaba da zama tare da masana'antar amma ba a matsayin jaruma ba. Zan zama mai bada umarni.
Amma kuma hakan ya danganta da yadda mijina yake so ya ganni; idan yace yana so na zauna a gida babu damuwa zan zauna.
Aminiya: Wani abu ne na bakin ciki da ya taba faruwa dake a wannan masana'anta?
Teema: Wani abu ya taba faruwa dani a lokacin ina sabuwar jaruma. Nayi kwanaki bakwai ana daukar mu a wani shirin fim, a lokacin har kunama sai da ta cije ni, amma a karshe aka ki biyana hakkina. Na sha wahala matuka a lokacin daukar wannan fim. Ina jin ba dadi a duk lokacin dana tuna da wannan lokaci.
Aminiya: Kina da wani sako ne ga da zaki bayyana ga masoyanki?
Teema: Ina so masoyana su san cewa babu wani abu da yake zama har abada, saboda haka ina so suyi amfani da damarsu a lokacin da suke da ita kafin ta wuce. Kuma ina so su cigaba da nuna mana soyayya, mu kuma munyi alkawarin ba za mu bari su ji kunya ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng