Gbajabiamila ya nada 'yan majalisar Kano 12 shugabannin kwamitoci a majalisar wakilai

Gbajabiamila ya nada 'yan majalisar Kano 12 shugabannin kwamitoci a majalisar wakilai

A ranar Alhamis, 24 ga watan Yuli, kakakin majalisar wakilai na Najeriya, Femi Gbajabiamila, yayi nadin ciyamomin da za su jagoranci kwamitai 105 daban-daban wajen gudanar da al'amura gwarwadon yadda suka rataya a wuyan majalisar.

Cikin jerin 'yan majalisar da suka samu nadin shugabanci, jihar Kano ta yi zarra tamkar yadda ta saba inda ta samu ciyamomi 12 fiye da kowace jiha a Najeriya kamar yadda jaridar Kano Today ta ruwaito.

Ga jerin sunayen 'yan majalisar Kano, kananan hukumomi da suke wakilta tare da kujerar mukami ta jagorancin kwamiti da Honarabul Gbajabiamila ya nada kamar haka:

1. Sha'aban Sharada (Kano Municipal) - Kwamitin tsaro da leken asirin kasa

2. Aminu Sulaiman Goro (Fagge) - Kwamitin makarantun gaba da sakandire.

3. Munnir Babba (Kumbutso) - Kwamitin kwalejan ilimin noma.

4. Mahmoud Abdullahi (Albasu/Gaya/Ajingi) - Kwamitin albarkatu da ma'adanan man fetur

5. Nasir Ali Ahmed (Nasarawa) - Kwamitin samuwa na kasa.

6. Ali Muhammad (Wudil/Garko) - Kwamitin masana'antu, samar da aiki da kwadago.

7. Abubakar Kabir Abubakar (Bichi) - Kwamitin Ayyuka.

8. Kabiru Idris (Kura/Madobi/Garun Malam) - Kwamitin kungiyoyin ci gaban al'umma.

KARANTA KUMA: Dalibai 1.59m da sauran abubuwa 5 a kan sakamakon jarabawar WAEC ta bana

9. Mustapha Dawaki (Dawakin Kudu/Warawa) - Kwamitin gidaje da zamantakewa.

10. Alhassan Rurum (Rano/Kibiya/Bunkure) - Kwamitin Fansho.

11. Sani Bala (Kunchi/Tsanyawa) - Kwamitin biyan bukatun al'umma.

12. Tijja Bala Jobe (Tofa/Rimin Gado/Dawakin Tofa) - Kwamitin raya karkara.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel